Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Muhammad Abdulkadir ya rushe mambobin Majalisar zartaswa ta jihar da suka kunshi kwamishinoni da manyan masu ba shi shawara a bangarori daban-daban.
Wannan batun ya fito ne daga bakin sakataren Gwamnatin jihar Bauchi, Ibrahim Kashim yayin da ke ganawa da ‘yan jarida domin yi musu bayanin kan sakamakon ganawar Majalisar zartaswar jihar (SEC) ta karshe da ya gudana a ranar Alhamis.
A cewar sauran wadanda rushewar ta shafa sun hada da manya da kananan masu taimakawa da suka kunshi SSAs, SAs, PAs da sauran masu rike da mukaman siyasa da suke shugabantar ma’aikatu da rassan gwamnati daban-daban dukkaninsu gwamnan ya sallama.
Sai dai kuma ya ce, sakataren Gwamnatin jihar Ibramin Kasim, da shugaban ma’aikatan gidan gwamnati, Hassan Gamawa, da PPS za su cigaba da zama a kujerunsu har zuwa karshen kammala shirye-shirye kafa sabuwar gwamnati.
A cewar Ibrahim, a lokacin ganawar gwamna Bala Mohammed ya gode wa dukkanin mambobin Majalisar zartaswa tasa, ya jinjina da irin gudunmawar da kowa ya bayar wajen samun nasarar gwamnatinsa a zango na farko.
Idan za ku tuna dai Bala Muhammad ya sake samun nasarar tazarce a yayin zaben 2023 da aka gudanar wanda ya fito takara a karkashin jam’iyyar PDP, lamarin da ke nuni da cewa za a sake rantsar da shi a karo na biyu a ranar 29 ga watan Mayun da muke ciki.