Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Muhammad, ya sauke kwamishinoni biyar daga muƙamansu tare da zaɓar sabbin mutane takwas domin inganta harkokin mulki da kyautata hidimar al’umma.
Kwamishinonin da aka sallama su ne:
- Yadda Ambaliyar Ruwa Ta Mamaye Wasu Sassa A Makkah
- Fashewar Bam Ya Kashe Dalibi ɗaya, Ya Jikkata 4 Abuja
- Dakta Jamila Mohammed Dahiru (Ilimi)
- Barista Abubakar Abdulhameed Bununu (Tsaro Cikin Gida)
- Usman Danturaki (Watsa Labarai)
- Farfesa Simon Madugu Yalams (Ayyukan Gona)
- Alhaji Yakubu Ibrahim Hamza (Harkokin Addinai)
Kakakin gwamnan, Mukhtar M. Gidado ne, ya bayyana cewa wannan sauyin na da nufin kawo sabbin dabaru don magance ƙalubale da inganta shugabanci a jihar.
Ya kuma yi godiya ga waɗanda aka sallama bisa gudunmawar da suka bayar ga ci gaban Bauchi tare da musu fatan alheri a rayuwarsu.
Haka kuma, gwamnan ya tura sunayen sabbin mutane takwas ga majalisar dokokin jihar don neman amincewa da su a matsayin sabbin kwamishinoni.
Waɗannan sunayen sun haɗa da:
- Hon. Isa Babayo Tilde (Toro)
- Abdullahi Mohammed (Misau)
- Dr. Bala Musa Lukshi (Dass)
- Usman Usman Shehu (Shira)
- Iliyasu Aliyu Gital (Tafawa Balewa)
- Farfesa Titus Saul Ketkukah (Tafawa Balewa)
- Hon. Adamu Babayo Gabarin (Darazo)
- Dakta Mohammed Lawal Rimin Zayam (Toro)