Gwamnan Jihar Bauchi Bala Muhammad Abdulkadir, ya yi wa fursunoni 153 da suke zaune a gidan gyaran hali daban-daban a jihar afuwa.
Al’amarin ya gudana a cikin bukukuwan tunawa da samun ‘yancin kan Nijeriya shekaru 62 da suka gabata da aka gudanar.
- Gwamna Bala Ya Jinjina Wa Takwaransa Na Borno Kan Yaki Da Boko Haram
- Manufar Ganowa Da Kawar Da Cutar COVID-19 Nan Take Ta Kasar Sin Ta Yi Tasiri In Ji Babban Mashawarci Game Da Kiwon Lafiya
Bala Muhammad wanda ya samu cikakken ikon yin afuwa bisa dogara da sashin doka na 212 (1) da 2 na kundin tsarin mulkin kasa da ya ba shi damar yin afuwar.
Gwamnan wanda a kashin kansa ya dauki alhakin biyan tarar da kotuna suka yanke wa fursunonin, kuma ya bai wa kowane daga cikin ‘yantattun fursoninin kyautar Naira N50,000 domin su fara gudanar da sana’o’in dogaro da kai bayan sake komawarsu cikin al’umma.
Da ya ke mika kyautar kudin ga wadanda suka amfana a gidan gwamnatin jihar, gwamnan ya bayyana cewar afuwa ga fursunoni 153 da aka daure sakamakon aikata laifuka daban-daban ya gudana ne bisa doka da ta ba shi ikon yin hakan.
Ya ce, matakin na zuwa ne bayan shawarwarin da kwamitin afuwa da yafiya na jihar ya ba shi, wanda ya ce an duba laifukansu kuma an gano cewa za su zama mutane na kwarai kuma masu amfani a cikin al’umma.
Ya nuna damuwarsa na cewa wasu daga cikin fursunonin a kan dan kankanin kudin tara mutum sai ya shafe tsawon shekaru a daure.
Ya taya fursunonin da aka ‘yanta murna tare da jawo hankalinsu da cewa kada su koma rayuwarsu ta da, ko yin abubuwan da ka iya maidasu gidan yarin, ya nemi su zama mutane na kwarai a cikin al’umma domin jama’a ta amfanesu.
A nasa jawabin, shugaban kwamitin afuwa da yafiya na jihar Bauchi, kuma kwamishinan shari’a na Jihar Barista Abdulhamid Abubakar Bununu ya bayyana cewar an yi zabin wadanda aka yi wa afuwa ne bisa dacewa da cancanta.
Ya ce kudin tara da aka biya, gwamnan ne a kashin kansa ya biya, kuma dukkanin matakan da suka dace a dokance ya cika wajen samar da afuwa ga fursunonin.
Da yake jawabin godiya a madadin dukkanin fursunonin da aka ‘yanta, Saidu Adamu Giade, ya ce abun da gwamnan ya musu ba za su taba mancewa a cikin rayuwarsu ba, ya kuma ce tabbas za su tababtar ba su sake yin wasu laifukan da za su koma gidajen yarin ba.