Gwamnan Jihar Edo, Sanata Monday Okpebholo, ya dakatar da Dokta George Oshiapi Egabor, Okumagbe na Masarautar Uwano da ke Agenebode, a Ƙaramar Hukumar Etsako ta Gabas, saboda yawaitar sace mutane da kashe-kashe a yankinsa.
Dakatarwar ta fito ne ta bakin Babban Sakataren YaÉ—a Labaran Gwamnan, Fred Itua.
- 2027: Fastocin Takarar Shugaban Ƙasa Na Gwamnan Bauchi Sun Bayyana
- Tinubu Ya Komo Nijeriya Bayan Ziyarar Mako 3 A Turai
Bayanin ya bayyana cewa an yanke wannan hukunci ne saboda rahotannin da ke yawaita na aikata laifuka a yankin, wanda hakan ke haifar da fargaba da rashin kwanciyar hankali ga mazauna yankin.
Gwamnan ya ce dakatarwar wani ɓangare ne na matakan wanzar da zaman lafiya da inganta tsaro a yankin.
Sanarwar ta bayyana cewa an kama sakataren sarkin, Cif Peter Omiogbemhi.
An kama shi ne sakamakon wani mummunan al’amari da ya faru kwanan nan, wanda ya yi sanadin mutuwar wani babban bafadan masarautar, John Ikhamate, lamarin da ya tayar da ƙura da kira na ganin an samu adalci.
Gwamna Okpebholo ya tabbatar wa da jama’a cewa gwamnatinsa na da niyyar yaƙar rashin tsaro a faɗin jihar, tare da ɗaukar mataki kan shugabannin al’umma da suka gaza yin abin da ya dace a yankunansu.
Ya kuma buƙaci sarakunan gargajiya da su mara wa gwamnatinsa baya wajen tabbatar da zaman lafiya da haɗin gwiwa da jami’an tsaro.
Gwamnatin jihar ta kuma buƙaci al’ummar Masarautar Uwano da su kwantar da hankalinsu tare da bin doka yayin da bincike ke gudana kan lamarin kisan.
Haka kuma ta gargaɗi duk wani shugaba da aka samu da hannu a aikata ko ɓoye laifuka zai fuskanci hukunci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp