Gwamnan jihar Edo, Sanata Monday Okpebolo, ya amince da kafa wani kwamiti karkashin ma’aikatar tantance kadarorin jihar mai mutum 14 da zai binciki gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Godwin Obaseki.
Wata sanarwa da Babban Sakataren Yada Labaran gwamnan, Fred Itua ya sanya wa hannu a safiyar Lahadi, ta ce matakin na da matukar muhimmanci a kokarin da Gwamnan ke yi na dora Jihar a kan turbar ci gaba da shugabanci mai rikon amana.
Gwamna Okpebholo zai kaddamar da kwamitin a ranar Talata, 26 ga watan Nuwamba, 2024, a gidan gwamnati da ke birnin jihar, Benin.