Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bada umarnin rufe dukkannin gidajen casu da raye-raye da aka fi sani da gidajen ‘Gala’ a jihar.
Sakataren Gwamnatin Jihar Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi ne ya sanar da umarnin a ranar Litinin, ya ma mai cewa matakin ya biyo bayan jerin korafe-korafen da jama’a ke yi ne game da badala da aikata miyagun laifuka dama haddasa matsalar tsaro da ake samu a irin waɗannan gidaje na casu in dare ya yi.
Don haka Gwamnan ya umarci rundunar ‘yansanda da jami’an tsaron Civil Defence da kuma na Operation Hattara su kimtsa jami’ansu don aiwatar da wannan umarni tare da tabbatar da bin doka da oda sau da kafa.
Don kaucewa duk wani shakku, gidajen galan da abin ya shafa su ne: Jami’a Gidan Wanka da ke Mil 3 Sabuwa, da gidan wasan kwaikwayo na White House (Babban Gida) da ke sabuwar Mil ukun kan hanyar Yola; da Gidan Lokaci General Merchant dake Mil 3 hanyar Reservoir, da kuma Farin Gida Entertainment II dake Wuro Karal kan hanyar Kalshingi.
Sauran su ne: Gidan Zamani Entertainment dake Tumfure kan hanyar Yola; da Albarka Entertainment dake Wuro Karal a Bypass kusa da Hara Form; da Gidajen Gala dake Garin Kuri, da Kauyukan Luɓo da Kurɓa duk a Karamar Hukumar Yamaltu Deba.
Haka kuma umarnin ya shafi gidan gala na Turaren Wash dake Trailer Park Kan hanyar Bauchi, da Gidan Gala dake cikin Garin Bajoga a karamar Hukumar Funakaye.