Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya ƙaddamar da rabon riguna 30,000 ga ɗalibai mata a manyan makarantun sakandire da ke faɗin jihar. Taron rabon ya gudana ne a makarantar sakandiren kimiyyar mata ta gwamnati da ke Jahun, wanda ma’aikatar ilimi mai zurfi ta shirya.
Gwamna Namadi ya jaddada fifikon da gwamnatinsa take bayarwa kan ilimin yara mata, wajen samar da kayan sawa kyauta. Ya kuma bayyana cewa ilimi ga ƴaƴa mata a Jigawa kyauta ne tun daga matakin firamare zuwa manyan makarantu, inda ya nuna muhimmancin ilimi ga al’umma.Gwamnan ya kuma yi alkawarin inganta hanyoyin samun ilimi mai sauƙi da inganci.
- Ramadan: Gwamnatin Jigawa Za Ta Ciyar Da Mutum 171,900 A Kullum Da Azumi – Namadi
- Obi Na Jam’iyyar Labour Ya Yi Wata Ganawar Sirri Da Tsohon Gwamnan Jigawa Sule Lamido
Namadi ya bayyana cewa gwamnatinsa ta samar da yanayi mai kyau na ci gaban malamai, tare da himmatuwa wajen ci gaba da ba da horo da sake horarwa don inganta ayyukan koyo da koyarwa.
Kwamishinan ilimi mai zurfi na jihar Jigawa Malam Isa Yusuf, ya yabawa gwamnan bisa wannan shiri da yayi domin zai taimaka wajen zaman ɗalibai mata a makarantu. Ya ƙara da cewa gwamnan ya amince da gyara makarantun mata guda 12, da raba littafan motsa jiki 70,000, da kuma sayo injinan dinki domin taimakawa dalibai su samu sana’o’i daban-daban.
Shugabar ƙungiyar ANCOPSS ta jihar, Asmau Sulaiman, ta godewa gwamnan bisa tallafin da yake ba wa yara mata a fannin ilmin ƴaƴa mata, ta yadda kowace yarinya a Jigawa za ta iya zuwa makaranta.
Wasu daga cikin Waɗanda suka ci gajiyar shirin Safiya Danladi da Zainab Ibrahim sun bayyana godiyarsu tare da yin alƙawarin daukar karatunsu da muhimmanci.