Kasa da watanni shida da babban zaben 2023, gwamnan Jihar Bauchi Bala Muhammad ya nada sabbin kwamishinoni guda shida.
A wata sanarwar da ya fitar wa manema labarai a ranar Talata, hadimin kakakin Majalisar dokokin Jihar, Malam Abdul Ahmad Burra, ya ce gwamna Bala Muhammad ya aike wa Majalisar dokokin Jihar jerin sunayen kwamishinonin da ya zaban domin neman tantancewa da amincewarsu.
Burra ya bada sunayen kwamishinonin da aka zaba da cewa su ne: Abdulkadir Ibrahim (Karamar Hukumar Alkaleri), Zainab Baban Takko (Karamar Hukumar Bauchi), Adamu Babayo Gabarin (Karamar Hukumar Darazo), da Maryam Garba Bagel (Karamar Hukumar Dass).
Sauran su ne: Dakta Sabiu Abdu Gwalabe (Karamar Hukumar Katagum) da kuma Ahmed Aliyu Jalam da ya fito daga karamar hukumar Dambam.
Kazalika, gwamnan ya kuma bukaci Majalisar da ta tantance tare da amincewa da Mista Joshua Titus Sanga a matsayin darakta-janar na hukumar ‘Public Procurement Bureau’ gami da Mista Sagir Abdullahi Muhammad a matsayin babban Mai binciken kudade na jihar (Auditor General).
A cewar sanarwar, nadin Sanga da Muhammad Majalisar ta tura bukatar nasu zuwa ga kwamitocinta na kasafi da na kula da dukiyar al’umma domin tantancesu kana an basu makonni biyu da su kammala aikinsu.
Burra ya kara da cewa Majalisar ta ware ranar 7 ga watan Satumban 2022 a matsayin ranar tantance kwamishinonin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp