Gwamna Jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ya rasu bayan ya sha fama da jinya.
Wata majiya daga iyalinsa ta shaida wa manema labarai a ranar Laraba cewa Akeredolu ya rasu a Legas.
- Tinubu Ya Yi Allah-Wadai Da Harin ‘Yan Ta’adda A Filato
- Tinubu Ga Gwamnoni: Dole Ne Mu Tabbatar Da Zaman Lafiya A Nijeriya
Leadership Hausa ta samu labarin cewa likitocin gidan gwamnati ne suke kula da shi har lokacin da ya rasu saboda ba za su iya kai shi kasar waje ba.
“Akeredolu ya rasu; Ya rasu a Legas,” in ji majiyar.
Yana da shekaru 67 a duniya.
Gwamnan da ke fama da rashin lafiya ya dawo Nijeriya ne a watan Satumba bayan hutun jinya na watanni uku a Jamus.
Ya dawo ofishinsa bayan da shugaba Bola Tinubu ya umarce shi da ya mika mulki ga mataimakinsa, Lucky Aiyedatiwa.
Mataimakinsa, Aiyedatiwa ya ya rike mulkin jihar na tsawon lokacin da gwamnan ya yi jinya.
Bayan dawowarsa Nijeriya a watan Satumba, Akeredolu ya zauna a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo kuma ya yi kokarin gudanar da mulkin jiharsa daga nan, lamarin da ya fusata jama’a da dama a Jihar.