Gwamnan jihar Kadauna, Sanata Uba Sani ya kaddamar da dakunan kwanan dalibai mai dauke da gadaje 400 a makarantar sakandiren mata ta gwamnati da ke Kawo da kuma katafaren ofishin hukumar raya birnin Zariya.Â
Da yake jawabi a wajen kaddamar da ginin, Gwamna Uba ya bayyana ce wa, kammala aikin ginin kwanan daliban na daya daga cikin alkawuran da ya dauka na fifita ilimi a lokacin yakin neman zabe.
A shekarar 2020 da ta gabata ne, dakunan daliban suka yi gobara, Gwamnan, ya nuna farin cikinsa da sake gina dakin kwanan daliban tare da gina karin ajujuwan karatu da nufin sake inganta ilimin yara mata.
Da take jawabi, shugabar makarantar GGSS Kawo, Kaduna, Misis Victoria Hassan ta bayyana jin dadin ta kan kaddamar da dakunan da ajujuwan makarantar da Gwamna Uba Sani ya yi.
Hakazalika, Gwamna Uba Sani ya kuma kaddamar da katafaren ginin hukumar raya birnin Zariya.
A cewarsa, hukumar kula da birnin Zariya, za ta yi aiki ne kamar yadda takwarorinta na Kaduna da Kafanchan suke yi, an tsara su bisa irin tsarin takwararsu mai kula da birnin Abuja, domin su dinga kula da gari da gudanar da ayyuka, kamar gina tituna, kula da shara da kuma daidaita yanayin kasuwanci a yankin.
Ya nanata kudirin gwamnatinsa na ganin jihar Kaduna ta samu ci gaba cikin gaggawa, inda ya bayyana cewa, ba zai yi kasa a guiwa ba a kokarin da yake yi na sake inganta ababen more rayuwa da bunkasa tattalin arzikin jihar.
Tun da farko, shugabar hukumar raya birnin Zariya, Hajiya Balaraba ta bayyana cewa, tun bayan kafa hukumar, ta gudanar da ayyuka da dama kamar gina tituna da zamanantar da birnin tare da hadin guiwar hukumomin KADGIS, KASUPDA da sauran hukumomi.
Kazalika, hukumar ba a barta a baya ba wajen kwashe shara a birnin Zariya.