Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta dage shari’ar da ta ke sauraro har zuwa 6 ga watan Satumbar wannan shekara da muke ciki, wadda wani Limamin Masallacin Juma’a mai suna Imam Ibrahim Lawan ya shigar gabanta, inda yake zargin Sanata Ali Ndume da Mansur Jarkasa, a matsayin wadanda ke da hannu wajen tura guggun matasa ‘yan ta’adda su ci zarafinsa tare da yi masa mummunan rauni. Kazalika, ya zargi wadanda yake karar da cewa, sun hada ayarin ‘yan ta’addan ne da nufin hallaka shi, a masallacin da yake gabatar da Limanci na ‘Yan Majalisu a Apo da ke Zone B cikin Birnin Tarayya Abuja.
Kafin mai shari’a M. Muazu ya kai ga tsayar da ranar yanke hukuncin, ya baiwa Lauyan da ke kare wadanda ake zargin, wato Sanata da Mansir Jarkasa da kuma Jami’in ‘Yansanda (CSP) Ibeh Chukwudi, damar kalubalantar karar da aka shigar a gaban Kotun.
- Sin Ta Fara Shirin Aikewa Da Sinawa Zuwa Duniyar Wata Nan Zuwa 2030
- Rage Radadin Cire Tallafi: Gwamnati Ta Baiwa Kowacce Jiha Naira Biliyan Biyu A Kashin Farko
Kafin nan, an gabatar da shaidar da matar Limamin ta bayar mai suna Shamsiyya, inda ta bayyana cewa a ranar 16 ga watan Yunin 2023, Ndume ya yi sallah a wannan masallaci, ana kuma idarwa ne sai ya tashi ya fice daga masallacin a fusace, bisa zargin nasihar da Liman zai gabatar, ta shafe shi ne kai tsaye.
Ta kara da cewa, “wanda a wannan lokaci, Liman ya yi kira kai tsaye ne tare da nusasshe da mutane a kan muhimmancin neman ilmi tare da aiki da shi, bisa koyarwar Alkur’ani da bin sunnar Annabi Muhammad SAW. Amma sai ga shi daga bisani Sanata ya dawo wannan masallaci yana kumfar baki da zage-zage tare da cin zarafinsa.”
Kamar yadda yake a rubuce a Kotu, wannan Uwargidan Liman ta hakikance cewa, ranar Lahadi wadda ta yi daidai da 18 ga watan Yunin wannan shekara, Maigidan nata (Liman) yana haramar tayar da Sallar La’asar a matsayinsa na Babban Limamin Masallacin, sai Ndume da Jarkasa tare da rakiyar guggun wasu mutane, suka fizge lasifikar da ke hannunsa suna kuma yi masa gargadi cewa, an dakatar da shi a matsayinsa na Babban Limamin wannan masallaci.
“Ganin faruwar hakan ya yi matukar ba shi mamaki da al’ajabi, inda ya dage sai ya aiwatar sallar abinsa kamar yadda ya saba, amma sai wani daga cikin dattawan masallacin ya ba shi shawara tare da jan hankalinsa nacewan ya yi hakuri ya fice daga masallacin don gudun tashin hankali, nan take ya dauki wannan shawara ya kuma fice daga masallacin,” in ji ta.
A cewar tata, ganin haka ne yasa Maigidan nata ya garzaya Ofishin ‘Yansanda na Apo, don shaida musu abin da ke faruwa domin gudun abin da ka je ya zo. Dawowar sa ke da wuya, “kafin ya ankara, gungun wasu matasa ‘yan ta’adda karkashin jagorancin Sanata Ndume da Jarkasa, suka far masa tare da dukan sa babu ji babu gani, wanda hakan ya yi sanadiyar samun mummunan rauni a kansa.”
Wannan dalili ne ya sa, Lauyan mai kara (Liman), Al-bashir Lawal Likko, ya nemi wannan Kotu da ta dubi irin wannan cin zarafi da keta haddi da zalinci da kuma mummunan raunin da aka yi wa wannan mai kara, wanda ko shakka bau ya saba wa doka da kuma kundirin tsarin mulkin wannan kasa, a yi masa adalci tare da kwato masa ‘yanci na wannan mummunan zalinci da aka yi masa.
Lauyan ya kara da cewa, lokacin da aka shigar da rahoto a Ofishin ‘Yansanda na Apo, wanda yake karewa (Liman) da wasu wadanda ke tare da shi, sai aka bi su duka aka kame wai da sunan masu kokarin tayar da tarzoma a tsakanin al’umma, aka kuma gurfanar da su a Kotun Magistiri da ke Abuja.
Sai kuma a bangaren wadanda ake karar, ma’ana Sanata Ndume da Jarkasa, Lauyansu Ben Jones Akpan, ya nemi Kotun ta yi watsi da kara a matsayin wani batu mara tushe da kan gado.
Har wa yau, ya bayyana wa Kotun cewa tuni kwamatin wannan masallaci ya dakatar Limamin, sakamakon zargin sa da ake yi da rashin gudanar da al’amuran masallacin yadda ya kamata da kuma barin wadanda ba su dace ba, marasa kuma alaka da masallacin su rika kwana a ciki, wanda hakan ya saba wa dokar masallacin.
Yanzu haka dai, Kotun ta dage shari’ar tare da tsayar da ranar 6 ga watan Satumbar wannan shekara a matsayin ranar yanke hukuncin. Inda mai karar ke ci gaba da ikrarin cewa, yana nan a kan bakarsa na kokarin neman hakkinsa, babu gudu babu ja da baya.