Alhaji Sabo Yusuf Faru (Dan Isan Faru), ya bayyana cewa kafa kamfanoni da gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya yi a wasu sassan jihar da Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya kaddamar a kwanakin bayar, alamu ne da nuna cewa gwamnan ya yunkura domin warware matsalolin rashin aikin yi ga matasa a jihar.
Dan Isan ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Zariya.
Ya kara da cewa wanna matakin samar da kamfanoni da kuma cibiyoyin koyon sana’o’i alamu ne da suke nuna Gwamnan Sani ya fara daukar matakan warware matsalolin da suke addabar matasa a Jihar Kaduna.
- Majalisa Ta Yi Allah-wadai Da Kashe Wasu Matafiya ‘Yan Kaduna 13 A Jihar Filato
- Tinubu Ya Ƙaddamar Da Asibiti, Motocin Bas Na CNG A Kaduna
A cewarsa, mataki na gaba da ya dace gwamnan Jihar Kaduna ya dauka shi ne, yin tsari mai inganci ga matasa da aka koya wa sana’o’i, ta yadda za su ci gaba da yin sana’o’i da aka koya masu a cibiyoyin da aka samar.
Dan Isan ya ce yin hakan zai sa gwamnati ta zama mai daraja ga al’ummar Jihar Kaduna, ba a koya wa matasa sana’a a yaye su ba tare da yin ingantaccen shiri ko tsarin da zai sa a ce kwalliya ta biya kudin sabulu.
Alhaji Sabo ya yaba wa shugaban majalisar wakilai kuma Iyan Zazzau, Dakta Abbas Tajuddeen, na yadda a tsarinsa ake koya wa matasa sana’a da zarar sun kammala yana ba matasa kayayyaki da kuma kudade domin dogaro da kai.
Ya shawarci gwamnonin arewa da su duba matsalar durkushewar kamfanin yin tamfoli da ke Zariya, wanda a shekarun baya a fadin Nijeriya, wanna kamfanin ke yin tamfol da sojoji da kuma sauran al’umma ke amfani da sh a ayyuka daban- daban.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp