Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya yi alkawarin tallafa wa masu zanga-zangar #EndBadGovernance da aka yi wa afuwa, ta hanyar ba su aiki, horaswa kan sana’o’i, da jari ga wadanda suka kuduri aniyar zama na gari a cikinsu.
Sakataren Gwamnatin Jihar, Dr. Abdulkadir Muazu Meyere ne, ya bayyana cewa gwamnan ya nemi a kawo shaidar karatun wadanda suka kammala karatunsu domin ba su m ayyukan yi.
- Mene Ne CIIE Ke Kawowa Kamfanonin Kasashen Waje?
- Nijeriya Za Ta Kara Haɓaka Alaƙarta Da Sabon Zaɓaɓɓen Shugaban Amurka – Gwamnati
Wasu za su samu jari don fara sana’a, wasu kuma za a koya musu sana’o’i ko kuma a basu aiki.
Gwamnati za ta sa ido kan halayyar yaran 39 da aka saki kafin a basu karin tallafi.
An duba lafiyarsu, an ba su shawara game da zaman lafiyarsu, kuma an yi musu wa’azi kan muhimmancin zama mutane na gari.
Kowannensu an ba shi kyautar wayar salula da kudi Naira 100,000 a matsayin kyauta, sannan aks mayar da su gidajensu.