Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusif ya gabatar wa majalisa dokokin Jihar Kano kiyasin Kasafin Kudin Naira Biliyon 350 na Shekara ta 2024, inda sashin Ilimi ya samu kaso mafi tsoka na Naira Biliyon 95.
Gwamnan ya bayyana kasafin a matsayin kasafin kudin sake farfado da kimar Jihar Kano, Ya ce, hakan na cikin kokarin cika alkawuran da ya yi wa Kanawa a lokacin yakin neman zabe.
- Gwamnatin Kaduna Ta Mallaka Wa Rundujar Sojin Sama Fili Sama Da Hekta 43 Don Gina Gidaje
- Bamu Yarda Da Mulkin Wariya Ba A Falasdinu – Dakta Gumi
Ya ce akwai tazarar Naira biliyan 10, inda kudaden yau da kullum za su lakume Naira biliyan 134.4 wanda ke kashi 38 cikin dari na kasafin kudin.
Albashin ma’aikata shi ma zai lakume Naira biliyan 85.73, yayin da masu rike da mukaman siyasa tare da alawus-alawus da sauran bukatun yau da kullum suka samu Naira biliyan 78.4.
Da yake bayyana yadda kasafin kudin yake, Gwamna Abba Kabir Yusif ya ce, sashin Ilimi ya samu Naira biliyan 95.388 wanda ke zaman kaso 29.97 na jimlar kasafin kudin, sashin lafiya shi ma ya samu Naira biliyan 51.4, ma’aikatar ayyuka da gidaje ta samu Naira biliyan 40.4, sufuri Naira biliyon 4.8, tsare-tsare Naira biliyan 5.1 sai kuma harkar noma wadda aka ware wa Naira biliyan 11 sai kuma sauran kowane da abin da ya samu.
A karshe Gwamnan ya jinjina wa kokarin majalisar dokokin wanda ya ce duk cikin Gwamnonin kasar nan ba wanda ya kai shi jin dadin aiki da majalisar dokokinsa.