Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya mika wa majalisar dokokin jihar sunayen sunayen kwamishinoni shida da ya naɗa domin tantancesu zuwa ma’aikatu daban-daban.
Hakan na zuwa ne biyo bayan sauye-sauye da gwamnan ya yi a majalisar kwamishinoninsa a baya bayan nan inda aka dakatar da ofishin shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar tare da sallamar sakataren gwamnatin jihar Abdullahi Bichi da wasu kwamishinoni biyar.
- Minista Ya Buƙaci Jihohi Su Sake Tunani Kan Duk Wani Yunƙurin Rushe Ma’aikatun Yaɗa Labarai
- Hatsarin Jirgin Ruwa Ya Kashe Mutane 20, ‘Yan Kasuwa Da Yara A Benue
Kakakin majalisar, Ismail Jibrin Falgore, ne ya sanar da hakan a ranar Litinin yayin da yake karanta wasikar gwamnan a zauren majalisar.
Wadanda aka nada sun hada da Shehu Sagagi, Dr. Dahiru Mohd Hashim, Ibrahim Abdullahi Wayya, Dr Isma’il Dan Maraya, Gaddafi Sani Shehu da Abdulkadir AbdulSalam.
Sagagi shi ke rike da mukamin shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar a baya kafin dakatar da duk wasu harkokin ofishin.