Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta rage kuɗin aikin Hajjin 2025, saboda ƙalubalen tattalin arziƙi da ƙasa ke fuskanta.
Gwamnan ya yi wannan kiran ne yayin wani taro da Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano, ta shirya don raba Naira miliyan 375 ga alhazan da suka yi aikin Hajjin 2023.
- Cece-kuce Kan Badaƙalar Kuɗaɗe A NNPCL: SERAP Ta Bukaci Mele Kyari Ya Yi Bayani
- Yadda Ambaliyar Ruwa Ta Mamaye Wasu Sassa A Makkah
An dawo wa da alhazan kuɗin ne saboda matsalar wutar lantarki da ta faru a lokacin aikin Hajjin.
Babban Daraktan Hukumar, Alhaji Laminu Rabiu Danbaffa, ya tabbatar da cewa an dawowa da jihar kuɗaɗen ne don raba su ga alhazan da abin ya shafa.
Gwamnan ya yaba wa Gwamnatin Saudiyya da Hukumar NAHCON bisa saurin warware batun dawo da kuɗin.
Haka kuma, ya jinjina wa Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano, bisa kyakkyawan aikin Hajjin 2023, inda ya jaddada buƙatar ci gaba da wannan ƙwazon a nan gaba.