Gwaman jahar Kano Abba Yusuf, ya rantsar da mai shari’a, Dije Audu Aboki, a matsayin mace ta farko a mukamin Alkalin Alkalai ta jihar Kano.
Taron rantsar da Dije, ya gudana ne a ranar Litinin a dakin taro na Afirka da ke a fadar gidan gwamnatin jihar.
- Abba Gida-Gida Ya Bai Wa Alhazan Kano 6,166 Kyautar Miliyan 65
- Asibitin Yara Na Hasiya Bayero Zai Dawo Aiki – Abba Gida-Gida
Gwamna, Abba Yusuf, ya yi kira ga bangaren shari’a da su marawa gwamnatinsa baya wajen rutsa gine-ginen da aka yi a jihar ba bisa ka’ida ba, a kokarin da gwamnati ke yi na dawo da kadarorin gwamnatin jihar.
Kazalika, ya nanata mahimmancin da ke matakan gwamnati uku, inda ya ce, dangantar da ke tsakanin bangaren zartarwa da na shari’a, ba wai gasa ba ce, aikin ne na mara wa juna baya.
Ya yaba wa Dije Aboki kan aikinta, inda ya danganta ta a matsayin kwararriya mai kishin kasa, wanda hakan ya sa aka daga matsayinta zuwa Alkalin Alkalai ta jihar Kano.
Bugu da kari, gwamna Yusuf ya ce, akwai bukatar a rinka hukunta masu aikata manyan laifuka a jihar domin hakan ya zama izina ga sauran mutane masu tunanin aikata hakan.
A nata jawabin, Dije Aboki, ta godewa gwaman jihar bisa ba ta wannan damar, inda ta yi alkawarin yin gaskiya da adalci a shugabancin da za ta yi.
Aboki, ta yi alkawarin sake dawo da martabar bangaren shari’a na jihar, inda ta bukaci goyon bayan bangaren zartarwa na jihar da kuma na majalisar dokokin jihar.
Nadin na Dije Aboki, ya nuna yadda gwamnatin jihar ta dora dambar yin tafiya da matan jihar Kano a cikin kunshin gwamnatin jihar.