Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da korar mataimaka musamman guda biyu daga muƙamansu bayan kwamitocin bincike sun tabbatar da laifuffuka masu nauyi a kansu. Wannan mataki na zuwa ne bayan zarge-zarge da suka shafi sakin wani mai fataucin miyagun ƙwayoyi da kuma satar kayan tallafi.
Daga cikin waɗanda aka sallama akwai Abubakar Umar Sharada, Mataimaki na Musamman kan Shirye-Shiryen Siyasa, wanda kwamitin bincike ya gano shi a matsayin jagoran shirin sakin wanda ake zargi da fataucin miyagun kwayoyi, da Sulaiman Aminu Danwawu. Sharada an umurce shi da ya miƙa duk kayan gwamnati da ke hannunsa kafin ƙarshen ranar Litinin, 11 ga Agusta, 2025, kuma an gargaɗi shi kada ya yi sake ayyana kan shi a matsayin jami’in gwamnati a yanzu.
- Sai An Magance Matsalar Asusun Haɗin Gwiwa, Za A Tabbatar Da Cin Gashin Kan Ƙananan Hukumomi
- Sin Ta Gabatar Da Korafi Da Babbar Murya Dangane Da Kalaman Jagoran Philippines
Haka kuma, an sallami Tasiu Adamu Al’amin Roba, Mataimaki na Musamman na Ofishin Majalisar Zartarwa, ya fuskanci sallamar ne bayan kama shi da laifin sake sayar da kayan tallafi a shekarar 2024. An gurfanar da shi a gaban kotu kan zargin sata da haɗa baki, kuma an umurce shi ya mika duk dukiyoyin gwamnati da ke hannunsa kafin ranar 11 ga Agusta.
A gefe guda, gwamnatin jihar ta wanke Hon. Musa Ado Tsamiya, Mashawarci na Musamman kan Harkokin Magudanar Ruwa, daga duk wasu zarge-zarge da ake yi masa bayan kwamitin bincike ya tabbatar da rashin laifinsa.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sake jaddada ƙudurin gwamnatinsa na yaƙi da cin hanci da rashawa tare da jan hankalin duk jami’an gwamnati su kiyaye gaskiya da riƙon amana a aikinsu da rayuwarsu ta ƙashin kai.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp