Gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf ya taya jagoran jam’iyyar NNPP na kasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso murnar cika shekara 68 da haihuwa.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Gwamna Yusuf ya yaba da tasirin siyasar Kwankwaso da kuma gudummawar da yake bayarwa wajen ci gaban kasa, inda ya bayyana shi a matsayin jagora kuma jigo a fagen siyasar Nijeriya.
- Rundunar Soji Ta Ƙaryata Jita-jitar Mutuwar COAS Lagbaja.
- Yadda Muka Dakatar Da Yunkurin Tsige Ganduje Daga Shugabancin APC – Kungiyar Arewa Ta Tsakiya
“Ya mai girma Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, jagoranmu na jam’iyyar NNPP, ina taya ka murna cikarka shekara 68 da haihuwa,” in ji Yusuf.
Da yake magana kan alakarsa da Kwankwaso ta dimbin shekaru, Yusuf ya bayyana irin dimbin ilimi da gogewa da ya samu daga aiki da Kwankwaso cikin shekaru 38 da suka gabata.
A madadin iyalai da al’ummar jihar Kano, Gwamna Yusuf na yi wa tsohon gwamnan jihar Kano fatan alheri da samum nasara a acikin yi wa kasa hidima.