Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Dr. Abdullahi Umar Ganduje ta yafe wa wasu mutum 12 da aka yanke wa hukuncin kisa.
Sanarwar da mai magana da yawun gidan gyaran hali reshen jihar Kano, SC Musbahu Lawan Kofar Nassarawa ya fitar ta ce, wannan yana cikin shirin da gwamnatin take yi domin rage cunkoso a gidajen gyaran hali.
Sanarwar ta kara da cewa, gwamnan ya kuma rage hukuncin kisa da aka yanke wa wasu mutum shida zuwa hukuncin zaman gidan gyaran hali na din-din-din.
Har ila yau, gwamnan ya kuma yafe wa wasu mata su hudu, bayan da aka yanke musu hukunci mai tsawo sakamakon kyawawan dabi’un da suka nuna a tsawon zaman su a gidan.
Wasu daga cikin wadanda aka yafe wa dai sun shafe shekara 25 a kulle a gidan suna jiran a yanke musu hukunci.
Gwamnan kuma ya bayar da naira dubu biyar-biyar ga wadanda aka yafe wa domin su yi kudin motar tafiya gida.
Babban kwanturolan gidan gyaran halin na Kano, Sulaiman Muhammad Inuwa, ya gode wa gwamnan a kokarin sa na rage cunkoso a gidan gyaran halin sannan ya bukaci wadanda aka saka da su zama mutanen kirki kuma kada su sake aikata laifin da zaisa a sake mayar da su gidan.