Gwamnan jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf ya bayyana matukar alhininsa game da kisan Sadiq Gentle – babban dan jarida na musamman a ma’aikatar tarihi da al’adu, wanda ya rasu sakamakon raunukan da ya samu a wani harin da wasu da ake zargin ‘yan daba ne suka kai a kwanan nan.
A cikin sakon ta’aziyyar da mai magana da yawunsa, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya aike a ranar Alhamis, Gwamna Yusuf ya bayyana Gentle a matsayin “kwararre mai kwazo kuma mai kishin kasa” wanda mutuwarsa ta girgiza gwamnatin jihar da kafafen yada labarai.
- Ta Yaya Za a Ba Matasa Damar Raya Kansu?
- Yawancin ‘Yan Siyasar Nijeriya Ba Su Da Tarbiyya – Sarki Sanusi II
“Labarin rasuwar Malam Sadiq Gentle ya yi min zafi matuka,” in ji gwamnan.
Da yake la’antar kisan a matsayin “mummuna, dabbanci, kuma lamarin da ba za a lamunta ba,” gwamnan ya yi alkawarin tabbatar da adalci. Ya umurci hukumomin tsaro da su dau mataki tare da kama wadanda ke da hannu a kisan nasa nan take.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp