Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Raɗɗa, ya dakatar da wasu ma’aikatan gidan gyaran hali da ke Babbar Ruga, saboda laifin cin zarafi da azabtar da wani matashi mai suna Usman Musa, lamarin da ya kai ga yanke masa hannu.
Sanarwar da Sakataren Gwamnatin Jihar, Abdullahi Faskari, ya fitar ta bayyana cewa waɗanda aka dakatar sun haɗa da shugaban cibiyar, Abdulzahir Abubakar, mataimakinsa Bala Abubakar, da wani ma’aikaci mai suna Yunusu Yusuf.
- Abinda Ya Sa Ilimi Yake Da Muhimmanci Ga Rayuwar Al’umma (9)
- ‘Yansanda Sun Damke Mutum Shida Kan Kisan Da Aka Yi A Kasuwar Abuja
Gwamnan ya ɗauki wannan mataki ne bayan da kwamitin bincike da ya kafa ya kammala aikinsa tare da miƙa rahoto.
Binciken ya gano cewa ma’aikatan gidan sun nuna halin rashin tausayi da zalunci ga matasan da ke gidan gyaran halin.
Haka kuma, gwamnatin jihar ta kori wani ma’aikacin wucin gadi, Murtala Sulaiman, wanda aka samu da laifin dukan matashin da aka yanke wa hannu.
Gwamnatin ta ce ba za ta lamunci cin zarafi da amfani da iko ba da gangan wajen cutar da waÉ—anda ke cikin irin wannan cibiya ba.
Domin rage wa matashin raɗaɗi ta tallafa masa, gwamnatin jihar ta ba shi Naira dubu dari tara da saba’in (₦970,000) don yin magani, da kuma Naira miliyan 3.5 (₦3,500,000) domin sayen hannun roba da zai taimaka masa wajen yin rayuwa.
Gwamnan ya kuma amince da shirin sake fasalin cibiyar ta Babbar Ruga domin inganta ta da kuma hana irin wannan abu faruwa a nan gaba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp