Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda ya rage hutun da ya tafi domin ziyartar al’ummar Martau da ke karamar hukumar Malumfashi, wanda a baya-bayan nan ya sake fuskantar hare-haren ‘yan bindiga.
Gwamnan ya isa yankin ne da yammacin Larabar nan, inda nan take ya fara duba barnar da maharan suka yi, inda suka kashe mazauna yankin, da kona gidaje da matsugunansu.
- Nijeriya Za Ta Ɗaukaka Da Fasahar Ƙere-ƙere Da Tattalin Abinci – Tinubu
- Sin Ta Sanar Da Cimma Nasarar Dashen Huhun Alade A Jikin Bil’Adama
Radda, wanda a fili ya nuna kaduwarsa kan irin barnar da aka yi, ya ce, ya zo ziyarar ne don jajanta wa wadanda abin ya shafa da kuma tabbatar musu da cewa gwamnati ba za ta yi watsi da su ba a lokacin da suke bukatarta.
Ya yi alkawarin cewa, gwamnatinsa za ta kara hada kai da hukumomin tsaro domin dawo da zaman lafiya, tare da samar da kayayyakin agaji da tallafi ga wadanda abin ya shafa.
Majiyoyin yankin sun ce al’ummar yankin sun sha fama da hare-hare akai-akai a ‘yan makonnin da suka gabata, lamarin da ya tilastawa mazauna yankin kauracewa gidajensu.
Ku tuna cewa, Gwamna Radda a ranar 18 ga Agusta, 2025 ya bar kasar don hutun makonni uku domin duba lafiyarsa a kasar waje.
Gwamnan ya samu rakiyar manyan jami’an gwamnati da shugabannin hukumomin tsaro na jihar da kuma kungiyoyin bayar da agajin gaggawa ga al’umma.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp