Sabon Gwamnan Jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa ya dakatar da dukkanin Kwamishinonin jihar baki daya nan take.
Wannan na cikin wata sanarwa da sakataren yada labaransa, Prince Ebenezer Adeniyan, ya fitar a ranar Laraba.
- Amurka Za Ta Tallafa Wa Yammacin Afrika Da Dala Miliyan 45 Don Yaki Da Ta’addanci
- AFCON 2023: An Samu Daukewar Wutar Lantarki A Wasu Yankunan Kasar Cote d’Voire Sakamakon Shan Kashi
Sanarwar ta umarci dukkanin Kwamishinonin da manyan sakatarori gwamnatin jihar da su sauka kan mukamansu nan take.
Sanarwar ta kara da cewa gwamnan ya kuma umarci dukkanin masu bai wa tsohon gwamnan da ya rasu, marigayi Rotimi Akeredolu shawara da su ajiye mukamansu.
A watan da ya gabata ne Leadership Hausa, ta ruwaito yadda gwamnan ya rasu bayan fama da rashin lafiya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp