Bayan da Majalisar Dokokin Jihar Oyo ta tsige mataimakin gwamnan Jihar, Injiniya Rauf Olaniyan, Majalisar ta amince da zabin Shugaban hukumar kula da gidaje na jihar, Adebayo Lawal, a matsayin sabon mataimakin gwamnan Jihar.
Matakin ya biyo bayan aikewa da sunan Lawan da gwamnan Jihar Seyi Makinde ya yi wa Majalisar ne da neman goyon bayan Majalisar don amincewa da shi a ranar Litinin.
Ba tare da bata dogon lokaci ba da Majalisar ta bi matakan tsige mataimakin gwamnan Jihar ne ta Kuma amince da zabin Lawal din don ya maye gurbin sa.
Kakakin Majalisar Dokokin Jihar, Adebo Ogundoyin, wanda ya karanta wasikar da gwamnan ya aike wa Majalisar mai dauke da kwanan wata 18.
Idan za a iya tunawa dai kwanan nan ne gwamna Makinde ya ayyana sunan Lawal a matsayin abokin takararsa a 2023..
Da yake kare zabin Lawal din, Shugaban masu rinjaye na majalisar Sanjo Adedoyin, ya ce akwai bukatar su amince da zabin bisa dacewar wanda aka nada lura da irin gudunmawar da ya bayar wa cigaban jihar.
Da yake mara baya wa kudurin, Kazeem Olayanju, mamba mai wakiltar mazabar Irepo/Olorunsogo a Majalisar jihar ya nemi mambobin majalisar da su amince da zabin Lawal a matsayin sabon mataimakin gwamnan Jihar Oyo.
Nan take dai Majalisar ta amince da kudurin na amincewa da Lawal a matsayin sabon gwamnan Jihar
Bayan hakan Majalisar ta dage zamanta har sai ranar Alhamis 21 ga watan Yulin 2022.