Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu ya amince da sauya wa sakatarorin dindindin guda 25 ma’aikatu a fadin jihar.
Sauye-sauyen dai, na da nufin karfafawa tare da inganta ayyukan gwamnati a jihar.
- Harin Lakurawa: Shugaban Karamar Hukuma Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Sokoto
- Sabbin Dabarun Yaƙi Da Ta’addanci: Nan Ba Da Jimawa Ba, ‘Yan Ta’adda Za Su Ɗanɗana Kuɗarsu – COAS
An umurci sakatarorin da sauyin ya shafa da su kammala aikin mikawa da karbar ragamar aiki nan da ranar 6 ga Mayu, 2025, sannan su mika bayanansu ga ofishin shugaban ma’aikatan jihar.
Gwamnatin jihar ta ce, matakin na daya daga cikin kokarin gwamnati mai ci na inganta ayyukanta domin samar da romon dimokuraɗiyya ga al’ummar jihar Sokoto.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp