Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya bukaci sabbin sakatarorin dindindin guda 19 da su tunkari ayyukan da aka dora musu bisa gaskiya da adalci da kuma jajircewa.
Ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da jawabinsa bayan kammala rantsar da manyan sakatarorin a gidan gwamnati a Kaduna.
- Gwamnatin Kaduna Ta Nemi Saudiyya Ta Zuba Jari A Jiharta
- Gwamnan Kaduna Ya Bude Masaukin Dalibai Mai Gado 400 Da Ofishin Hukumar Raya Birnin Zariya
Gwamna Sani ya shaidawa sakatarorin cewa, fifita jin dadin al’ummar jihar Kaduna, shi ne abu mafi muhimmanci inda ya kara da cewa “mutane fa na kallon mu”.
“Bai kamata mu ba wa ‘yan jihar Kaduna wata kofa da za su yi kokonto kan alkawuranmu ba. Za mu ba ku duk gudunmawa da kwarin guiwar da kuke bukata don sauke nauyin da ke kanku cikin nasara. Amma duk da haka, muna bukatar biyayyarku da jajircewarku”
Gwamnan ya yi nuni da cewa, dukkan Sakatarorin kwararru ne a fanninsu, kuma za su sauke nauyin da ake bukata a kansu na aiwatar da manufofin gwamnatinsa da shirye-shiryensa yadda ya kamata.
Malam Uba Sani ya taya su murnar nadin da aka yi musu, ya kuma bukace su da su kara kaimi wajen sauke nauyin da ke kansu cikin adalci da jajircewa.
Gwamnan ya bukaci ‘yan uwa da abokan arziki da masu fatan alheri da su tallafa wa Sakatarorin da addu’a da karfafa guiwa.
An tura manyan sakatarorin su 19 zuwa ma’aikatu daban-daban domin gudanar da ayyukansu.