• English
  • Business News
Sunday, October 19, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnan Zamfara Ya Ƙara Mafi Ƙarancin Albashi Daga N7,000 Zuwa N30,000, Za A Fara Biya Daga Yuni

by Leadership Hausa
1 year ago
zamfara

Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya bayyana cewa gwamnatin sa za ta fara biyan mafi ƙarancin albashi na Naira Dubu Talatin a wata mai zuwa na Yuni.

Gwamnan ya yi wannan albashir ɗin ne a ranar Larabar nan a Lokacin da ya ke ganawa da shugabannin ƙungiyar ƙwadago ta jihar Zamfara.

A cikin wata sanarwa da Kakakin Gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris ya fitar yau a Gusau, ya bayyana cewa aiwatar da wannan mafi ƙarancin albashi ya nuna azamar gwamnatin jihar ne na kyautata jin daɗin ma’aikatan.

Sanarwar ta Idris ta ci gaba da ƙarin haske da cewa, gwamnatin jihar Zamfara za ta fara biyan mafi ƙarancin albashi na Naira Dubu 30, maimakon Naira 7,000 da suke karɓa, za a fara biya daga watan Yunin nan mai zuwa.

A lokacin da ya ke ganawa da shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago ta NLC da na Malamai ta TUC, Gwamna Lawal ya bayyana cewa fara biyan wannan mafi ƙarancin albashi na Naira Dubu 30, wani yunƙuri ne na ƙara wa ma’aikatan Zamfara azama.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Siyasa 11 Da Suka Faɗa Dambarwar Takardar Shaidar Karatu Ta Bogi

DHQ Ta Ƙaryata Rahoton Yunƙurin Yi Wa Tinubu Juyin Mulki

zamfara

“A yau, ina so in sanar da shugabannin ƙungiyar ƙwadago ta jihar Zamfara cewa gwamnati na za ta fara biyan mafi ƙarancin albashi na Naira dubu 30 a watan Yuni.

“Tun lokacin da na hau kujerar gwamnan jihar Zamfara, gwamnati na ta aiwatar da sauye-sauye da dama na jin daɗin ma’aikatan gwamnati domin tabbatar da walwalar su.

“Mun samu nasarar biyan albashin ma’aikata na watanni uku da aka riƙe, biyan kuɗin hutu da sauran alawus-alawus.

“Gwamnati na ta biya jimillar Naira Biliyan 4,337,087,490 a rukuni huɗu ga waɗanda suka yi ritaya daga matakin jiha da ƙananan hukumomi, waɗanda ba a biya su haƙƙoƙin su ba tun shekarar 2011.

“Muna da wasu tsare-tsare na inganta ayyukan ma’aikatan gwamnati a Zamfara. Babu wani ma’aikaci da zai yi fargabar yin ritaya, saboda za mu tabbatar da biyan kuɗin ritaya a kan kari ba tare da wani jinkiri ba. Mun himmatu wajen aikin jin daɗin al’umma.”

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Yadda Zargin Takardar Karatun Bogi Ta Tilasta Wa Minista Nnaji Murabus
Manyan Labarai

‘Yan Siyasa 11 Da Suka Faɗa Dambarwar Takardar Shaidar Karatu Ta Bogi

October 19, 2025
Tsadar Rayuwa Da Karuwar Ta’addanci Na Ci Gaba Da Tagayyara ‘Yan Nijeriya
Da ɗumi-ɗuminsa

DHQ Ta Ƙaryata Rahoton Yunƙurin Yi Wa Tinubu Juyin Mulki

October 18, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yansanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar Adawa Da Dokar Ta-ɓaci A Ribas
Tsaro

‘Yansanda Sun Kai Samame Maboyar ‘Yan Ta’adda, Sun Kwato Miyagun Kwayoyi A Gombe

October 18, 2025
Next Post
Sin Ta Nanata Wajibcin Kiyaye Fararen Hula Ta Hanyar Kawo Karshen Rikici

Sin Ta Nanata Wajibcin Kiyaye Fararen Hula Ta Hanyar Kawo Karshen Rikici

LABARAI MASU NASABA

Yadda Zargin Takardar Karatun Bogi Ta Tilasta Wa Minista Nnaji Murabus

‘Yan Siyasa 11 Da Suka Faɗa Dambarwar Takardar Shaidar Karatu Ta Bogi

October 19, 2025
gombe

Ɗaliban Jihar Gombe Sun Samu Ƙarin Kashi 100 Na Kuɗin Tallafin Karatu

October 18, 2025
Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

October 18, 2025
An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin

An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin

October 18, 2025
Tsadar Rayuwa Da Karuwar Ta’addanci Na Ci Gaba Da Tagayyara ‘Yan Nijeriya

DHQ Ta Ƙaryata Rahoton Yunƙurin Yi Wa Tinubu Juyin Mulki

October 18, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yansanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar Adawa Da Dokar Ta-ɓaci A Ribas

‘Yansanda Sun Kai Samame Maboyar ‘Yan Ta’adda, Sun Kwato Miyagun Kwayoyi A Gombe

October 18, 2025
Kamfanin Gine-Gine Na CCECC Ya Fara Gina Wani Titin Mota Da Zai Rage Cunkoso A Birnin Abuja Na Tarayyar Najeriya

Kamfanin Gine-Gine Na CCECC Ya Fara Gina Wani Titin Mota Da Zai Rage Cunkoso A Birnin Abuja Na Tarayyar Najeriya

October 18, 2025
ASUU

Cikin Wata 9 Farfesoshi 309 Sun Bar Aiki A Jami’o’in Gwamnati, In Ji ASUU

October 18, 2025
Masanin Ilimin Physics Chen Ning Yang Ya Rasu Yana Da Shekaru 103

Masanin Ilimin Physics Chen Ning Yang Ya Rasu Yana Da Shekaru 103

October 18, 2025
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

October 18, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.