• English
  • Business News
Friday, October 17, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnan Zamfara Ya Kaddamar Da Ofishin Kwamitin Amintattu Na Asusun Tsaro

by Leadership Hausa
2 years ago
zamfara

Gwamnatin Jihar Zamfara, ƙarƙashin Gwamna Dauda Lawal, ta ƙaddamar da ofishin amintattun Asusun Kula da Harkokin Tsaro domin daƙile ayyukan ’yan bindiga da sauran ta’addanci a jihar, inda Gwamnan ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na tallafa wa asusun ta kowane fanni.

A ranar Juma’ar Gwamna Lawal ya jagoranci ƙaddamar da ginin amintattun Asusun Kula da Harkokin Tsaro da ke Gusau babban birnin jihar.

A wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta ce asusun tsaron na Zamfara yana ƙarƙashin jagorancin Tsohon Sufeto Janar na ’yan sanda, MD Abubakar ne.

  • Yadda Rayuwata Ta Sauya Bayan Mayar Da Tsintuwar Naira Miliyan 15 – Auwalu

A cewar sanarwar, an ƙaddamar da aikin ne a ƙarƙashin wani kwamitin amintattu na ƙwararru a fannin tsaro domin aiwatar da aikin yadda ya kamata.

LABARAI MASU NASABA

Ranar Abinci Ta Duniya: NAWIA Ta Tallafawa Mata 114  Da Kayan Aikin Gona A Zamfara

Shugaban Ƙasa Zai Sake Nazari Kan Mutanen Da Aka Yi Wa Afuwa

A yayin bikin ƙaddamar da ginin, Gwamna Lawal ya buƙaci sauran jihohin ƙasar nan da su kafa irin waɗannan asusun amintattu, da daidaita tsare-tsare, da samar da tsarin da ya shafi tsaron yankin.

Ya ce, “Yayin da Asusun Tallafa wa Tsaro ya fara aiki cikin tsari, ina roƙon a haɗa hannu da irin waɗannan asusu da wasu jihohi ke kafawa a yankunan su domin haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen daƙile matsalar tsaro.

“Asusun yana da abubuwa da yawa da zai yi yayin da ya fara aiki. Wani abin da asusun zai ƙara mayar da hankali a kai shi ne tabbatar da cire wa yaranmu da matasanmu tunanin rikice-rikice da kuma nuna ƙabilanci, wanda hakan ke haifar da tayar da ƙayar baya a wasu al’ummomi. Wannan ya zama dole don samun ci gaba mai ma’ana kuma mai ɗorewa.

“A ƙarƙashin jagoranci mai nagarta na Shugaban Asusun, IGP M.D Abubakar (Mai Ritaya) da sauran jiga-jigan kwamitin amintattun, muna sa ido ga haɗin kanku don haɓaka rayuwar jama’armu nan take.

“Mun dogara da ku, domin mun san ku duka kuna da cancantar ɗaukar irin wannan nauyi. Na gode da hidimar ku da aikin ku ga jihar ku.

“Abin da ke faɗo min rai a duk lokacin da aka kai wani hari, shi ne yabo bisa ƙoƙarin da Rundunar Kare Jama’a ta Zamfara, wacce muka ƙaddamar kwanan nan take yi wajen ceto al’umma.

“Muna da niyyar ci gaba da ƙoƙari wajen haɗa kan al’umma, ci gaba da wayar da kan jama’a, da kuma tabbatar da bin ƙa’idojin aiki da dukkan mambobin Rundunar Kare Jama’a ta Zamfara suka rantse a kai.”

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

NAWIA
Labarai

Ranar Abinci Ta Duniya: NAWIA Ta Tallafawa Mata 114  Da Kayan Aikin Gona A Zamfara

October 16, 2025
Tinubu
Manyan Labarai

Shugaban Ƙasa Zai Sake Nazari Kan Mutanen Da Aka Yi Wa Afuwa

October 16, 2025
Gwamna Lawal Ya Yi Alhinin Kisan Jami’an Tsaro A Zamfara
Labarai

Gwamna Lawal Ya Yi Alhinin Kisan Jami’an Tsaro A Zamfara

October 16, 2025
Next Post
‘Yansanda Sun Cafke ‘Yammata Masu Yawon Dare A Yamai

‘Yansanda Sun Cafke ‘Yammata Masu Yawon Dare A Yamai

LABARAI MASU NASABA

Sin Da Afrika Sun Yi Alkawarin Tabbatar Da Nasarar Shirin TVET Na Nahiyar Afrika

Sin Da Afrika Sun Yi Alkawarin Tabbatar Da Nasarar Shirin TVET Na Nahiyar Afrika

October 16, 2025
NAWIA

Ranar Abinci Ta Duniya: NAWIA Ta Tallafawa Mata 114  Da Kayan Aikin Gona A Zamfara

October 16, 2025
Xi Ya Taya Hukumar FAO Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafuwa

Xi Ya Taya Hukumar FAO Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafuwa

October 16, 2025
Gaza

Wane Ci Gaba Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Gaza Ta Haifar?

October 16, 2025
Tsohon Ɗan Wasan Dambe, Ricky Hatton Ya Rataye Kansa

Tsohon Ɗan Wasan Dambe, Ricky Hatton Ya Rataye Kansa

October 16, 2025
Alkaluman Jin Ra’ayi na CGTN Sun Shaida Amincewar Al’umma Da Karfin Tattalin Arzikin Kasar Sin

Alkaluman Jin Ra’ayi na CGTN Sun Shaida Amincewar Al’umma Da Karfin Tattalin Arzikin Kasar Sin

October 16, 2025
Masu Bincike Na Sin Sun Kera Wani Dan Karamin Mutum Mutumin Hannu Da Zai Taimaka Wajen Gwaje-wajen Kimiyya

Masu Bincike Na Sin Sun Kera Wani Dan Karamin Mutum Mutumin Hannu Da Zai Taimaka Wajen Gwaje-wajen Kimiyya

October 16, 2025
Tinubu

Shugaban Ƙasa Zai Sake Nazari Kan Mutanen Da Aka Yi Wa Afuwa

October 16, 2025
Xi Jinping Ya Yi Kira Da a Kara Horar Da Kwararrun Masana A Fannin Aikin Gona

Xi Jinping Ya Yi Kira Da a Kara Horar Da Kwararrun Masana A Fannin Aikin Gona

October 16, 2025
Gwamna Lawal Ya Yi Alhinin Kisan Jami’an Tsaro A Zamfara

Gwamna Lawal Ya Yi Alhinin Kisan Jami’an Tsaro A Zamfara

October 16, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.