• English
  • Business News
Monday, August 4, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnan Zamfara Ya Samu Lambar Yabo Kan Ƙirƙiro Ayyukan Ci Gaba

by Leadership Hausa
1 year ago
in Labarai
0
Gwamnan Zamfara Ya Samu Lambar Yabo Kan Ƙirƙiro Ayyukan Ci Gaba
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya samu lambar yabo ta ‘Ƙirƙirar Ayyuka’ a bikin bayar da lambar yabo ta ‘Kyautar Yabo Ta Yi Wa Al’umma Hidima’ (NEAPS) bisa ɗimbin ayyukan da gwamnatinsa ta ƙaddamar da kuma kammalawa a cikin shekara guda.

NEAPS wani shiri ne na kamfanoni masu zaman kansu da kuma ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya (OSGF).

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta ce an gudanar da bikin karramawar na NEAPS ne a ranar Asabar da ta gabata a ɗakin taro na fadar gwamnatin tarayya.

  • Atiku Ya Koka Kan Yadda Matsalar Tsaro Ta Addabi ‘Yan Nijeriya

Sanarwar ta ƙara da cewa, mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, wanda ya wakilci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ne ya ba Gwamna Dauda Lawal lambar yabon.

Labarai Masu Nasaba

Gwamnatin Tarayya Ta Kwato ₦21bn, Ta Kashe Ƴan Ta’adda 78 — DG NOA

Yaran Gaza Suna Da Hakkin Rungumar Gobe

“A ranar Asabar ne aka karrama Gwamna Dauda Lawal da lambar yabo ta NEAPS saboda jajircewarsa na ƙoƙarin samar da nagartaccen sauyi, da kuma ƙoƙarin samar da al’ummar dimokuraɗiyya, da kuma gyara hukumomin gwamnati yadda ya kamata.

“Wasiƙar lambar yabon daga ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa an zaɓi Gwamnan Zamfara ne saboda ƙoƙarinsa wajen ƙirƙirar ayyukan ci gaban al’umma.

“An ba da lambar yabo ta shugaban ƙasar ne domin nuna godiya ga ƙoƙarin da gwamnatin Jihar Zamfara ke yi na ɓullowa da kuma kammala ayyuka da dama cikin shekara ɗaya.”

Gwamna Lawal ya nuna jin daɗinsa da karramawar, inda ya bayyana cewa hakan zai zama kwarin gwiwa ga ci gaba da ƙoƙarin ceto da sake gina Zamfara.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: ArewaAyyukaCi GabaGwamna Dauda LawalNijeriyaZamfara
ShareTweetSendShare
Previous Post

Majalisar Dokoki Na Shirin Yin Dokar Hukuncin Kisa Ga Masu Lalata Kadarorin Ƙasa

Next Post

Shugaban Kasar Sin Ya Aike Da Sakon Taya Murna Ga Taron Kare Muhalli Na Kungiyar Hadin Kai Ta Shanghai

Related

Gwamnatin Tarayya Ta Kwato ₦21bn, Ta Kashe Ƴan Ta’adda 78 — DG NOA
Labarai

Gwamnatin Tarayya Ta Kwato ₦21bn, Ta Kashe Ƴan Ta’adda 78 — DG NOA

56 minutes ago
Yaran Gaza Suna Da Hakkin Rungumar Gobe
Ra'ayi Riga

Yaran Gaza Suna Da Hakkin Rungumar Gobe

1 hour ago
Kwamitin Bincike Ya Miƙa Rahoto Kan Kwamishinan Sufuri Ga Gwamnatin Kano
Manyan Labarai

Kwamitin Bincike Ya Miƙa Rahoto Kan Kwamishinan Sufuri Ga Gwamnatin Kano

2 hours ago
Ruwan Wuta Ne Kawai Maganin ‘Yan Ta’adda Ba Sasanci Ba – Mataimakin Gwamnan Zamfara
Labarai

Ruwan Wuta Ne Kawai Maganin ‘Yan Ta’adda Ba Sasanci Ba – Mataimakin Gwamnan Zamfara

3 hours ago
Gwamna Buni Ya Bukaci Sabon Sarkin Gudi Ya Jagoranci Zaman Lafiya, Hadin Kai, Da Ci Gaban Kasa
Labarai

Gwamna Buni Ya Bukaci Sabon Sarkin Gudi Ya Jagoranci Zaman Lafiya, Hadin Kai, Da Ci Gaban Kasa

4 hours ago
Gina Tituna A Karkara Yana Bunkasa Tattalin Arziki – Gwamna Sule
Labarai

Gina Tituna A Karkara Yana Bunkasa Tattalin Arziki – Gwamna Sule

5 hours ago
Next Post
Shugaban Kasar Sin Ya Aike Da Sakon Taya Murna Ga Taron Kare Muhalli Na Kungiyar Hadin Kai Ta Shanghai

Shugaban Kasar Sin Ya Aike Da Sakon Taya Murna Ga Taron Kare Muhalli Na Kungiyar Hadin Kai Ta Shanghai

LABARAI MASU NASABA

Xi Jinping Ya Ba Da Muhimmin Umarnin Jin Ra’ayoyin Masu Amfani Da Intanet Kan Tsara Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar-Biyar Na 15

Xi Jinping Ya Ba Da Muhimmin Umarnin Jin Ra’ayoyin Masu Amfani Da Intanet Kan Tsara Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar-Biyar Na 15

August 4, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Kwato ₦21bn, Ta Kashe Ƴan Ta’adda 78 — DG NOA

Gwamnatin Tarayya Ta Kwato ₦21bn, Ta Kashe Ƴan Ta’adda 78 — DG NOA

August 4, 2025
Yaran Gaza Suna Da Hakkin Rungumar Gobe

Yaran Gaza Suna Da Hakkin Rungumar Gobe

August 4, 2025
Kwamitin Bincike Ya Miƙa Rahoto Kan Kwamishinan Sufuri Ga Gwamnatin Kano

Kwamitin Bincike Ya Miƙa Rahoto Kan Kwamishinan Sufuri Ga Gwamnatin Kano

August 4, 2025
Ruwan Wuta Ne Kawai Maganin ‘Yan Ta’adda Ba Sasanci Ba – Mataimakin Gwamnan Zamfara

Ruwan Wuta Ne Kawai Maganin ‘Yan Ta’adda Ba Sasanci Ba – Mataimakin Gwamnan Zamfara

August 4, 2025
Gwamna Buni Ya Bukaci Sabon Sarkin Gudi Ya Jagoranci Zaman Lafiya, Hadin Kai, Da Ci Gaban Kasa

Gwamna Buni Ya Bukaci Sabon Sarkin Gudi Ya Jagoranci Zaman Lafiya, Hadin Kai, Da Ci Gaban Kasa

August 4, 2025
Gina Tituna A Karkara Yana Bunkasa Tattalin Arziki – Gwamna Sule

Gina Tituna A Karkara Yana Bunkasa Tattalin Arziki – Gwamna Sule

August 4, 2025
Tsohon Dan Majalisar Taraba Usman Ya Fice Daga APC

Tsohon Dan Majalisar Taraba Usman Ya Fice Daga APC

August 4, 2025
Yadda Al’ummar Da Ke Zaune Da ‘Yan Bindiga Ke Rayuwa A Zamfara

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Da Dama A Kauyukan Zamfara

August 4, 2025
Gwamnatin Kano Za Ta Mayar Da Gidan Gyaran Hali Na Kurmawa Gidan Tarihi

Gwamnatin Kano Za Ta Mayar Da Gidan Gyaran Hali Na Kurmawa Gidan Tarihi

August 4, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.