Hukumar aikin Hajji ta kasa (NAHCON), ta sanar da cewa gwamnatin tarayya ba za ta iya ci gaba da biyan tallafi aikin hajjin ba kamar yadda ta saba ta hanyar karyar wa maniyyata farashin dala a babban bankin ƙasar nan CBN.
Mai magana da yawun hukumar, Fatima Sanda Usara, ce ta shaida haka cikin wata sanarwa da ta fitar, inda ta ce gwamnati ta daina bai wa maniyyata tallafin rangwamen farashin dala a jihohi da tarayya.
- Muna Tattaunawa Don Ganin An Tsagaita Wuta A Yakin Gabas Ta Tsakiya – Kamala HarrisÂ
- Yadda Muka Sanya Tinubu Ya Soke Kwangilar Aikin Hanyar Kankara Zuwa Katsina – Ibrahim MasariÂ
Tuni dai masana harkokin aikin Hajji a Nijeriya suka fara tsokaci game da yadda aikin hajjin baÉ—i na 2025 zai kasance sakamakon cire hannun gwamnati daga wanda suka yi hasashen kuÉ—in aikin Hajjin 2025 ka iya kai wa miliyan 10 ko fiye.
Sun bayyana cewa idan aka tafi a haka yadda farashin dala je tashin gwauron zabi, a yanzu kuÉ—in kujerar zai iya kai wa naira miliyan 10 ko ma iya fin hakan idan dalar ta tashi kamar yadda ya faru a baya.
Sun yi kira ga gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki kan harkokin aikin Hajjin da su Æ™ara duba lamarin don sauÆ™aÆ™a wa al’umma da ke burin zuwa sauke faralin a Æ™asa mai tsarki.