Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya jaddada cewa gwamnati da kafafen yaɗa labarai abokan hulɗa ne wajen gina ƙasa, ba ‘yan adawa ba, duk da saɓanin da ake samu a wasu lokuta.
Ya bayyana haka ne a yayin ziyarar ban-girma da tawagar gudanarwar kamfanin jaridun The Guardian suka kai ofishin sa ranar Alhamis.
- Gwamnonin Arewa Sun Nemi Gwamnatin Tarayya Ta Shawo Kan Matsalar Wutar Lantarki
- Mene Ne Ainihin Abun Da Philippines Ta Samu Daga Wajen Amurka?
“Ban yi imani da cewa gwamnati da ‘yan jarida ‘yan adawa ne ba, a’a, abokan hulɗa ne a cikin wannan aiki mai wuyar gaske na gina ƙasa, aikin da ke zuwa da mabanbantan ra’ayoyi da hanyoyi daban-daban,” inji Idris.
Ya bayyana irin rawar da kafafen yaɗa labarai ke takawa a matsayin masu sa ido kan al’umma, inda ya jaddada aikinsu na tabbatar da dimokuraɗiyyar Nijeriya, zaman lafiya, da haɗin kai, waɗanda ke da muhimmanci ga martabar ƙasar a duniya.
Ministan ya kuma amince da The Guardian a matsayin babbar kafar yaɗa labarai, wanda tarihi ya danganta da gwagwarmayar dimokraɗiyyar Nijeriya da yaƙi da mulkin soja.
Ya buƙaci jaridar da ta ci gaba da jajircewarta kan manufofin dimokuraɗiyya da kuma yin watsi da duk wani tasiri da zai kawo barazana ga zaman lafiyar ƙasa.
Idris ya kuma bayyana cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta mayar da hankali ne kan kawo sauyi a fannin zamantakewa da tattalin arziƙin Nijeriya.
Da yake mayar da martani, Babban Jami’in The Guardian, Toke Ibru, ya tabbatar da aniyar ƙungiyar na inganta haɗin kai, zaman lafiya, da tsaro, tare da bayyana rawar da take takawa a matsayin babbar murya a ci gaban dimokuraɗiyyar Nijeriya.
Sauran waɗanda suka halarci taron sun haɗa da Muƙaddashin Babban Sakatare na Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Misis Comfort Ajiboye, tare da wasu manyan jami’an gudanarwar The Guardian, da suka haɗa da Martins Oloja, Dr. Oluwafemi Adekoya, da Chuks. Nwanne.