• English
  • Business News
Tuesday, July 29, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnati Na ɗaukar Matakai Don Rage Farashin Abinci Ta Hanyar Zuba Jari A Noma – Minista

by Sulaiman
6 months ago
in Manyan Labarai
0
Gwamnati Na ɗaukar Matakai Don Rage Farashin Abinci Ta Hanyar Zuba Jari A Noma – Minista
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Gwamnatin Tarayya ta jaddada ƙudirin ta na rage farashin kayan abinci ta hanyar zuba jari mai yawa a fannin noma.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan a ranar Talata a Abuja yayin wani taron manema labarai da ya buɗe zaman bayar da rahoton ayyukan ministoci na shekarar 2025.

  • Sin Ta Ayyana Matakan Bunkasa Harkokin Sayayya Da Zuba Jarin Waje
  • Al’ummomi 44 Sun Yi Zanga-zangar Rashin Samun Wutar Lantarki Na Tsawon Shekara Daya A Kwara

Ya jaddada cewa ko da yake gwamnati ba za ta ƙayyade farashin abinci ba, tana ƙoƙarin rage farashi ta hanyar haɓaka samar da amfanin gona.

Labarai Masu Nasaba

Jami’an Tsaron Katsina Sama Da 100 Sun Rasu A Yaƙi Da ‘Yan Ta’adda – Gwamnati

Tinubu Ya Karrama Mata ‘Yan Ƙwallon Nijeriya Da Lambar Girmamawa (OON), Dala Dubu 100 Da Gidaje

Ya ce: “A baya, muna da wasu hukumomi da ke ƙayyade farashin kayan abinci, amma domin kasuwanci na ’yanci da bunƙasa harkokin noma, gwamnati ba ta ga dacewar ci gaba da hakan ba.

“Yanzu abin da gwamnati ke yi shi ne ta tabbatar da cewa ana samar da isassun kayan abinci, domin idan abu yana da yawa, farashin sa yana sauka da kan sa.”

Ministan ya kuma bayyana nasarorin da aka samu a fannin tsaro, inda ya ce a shekarar 2024 jami’an tsaro sun kashe ’yan ta’adda da ’yan bindiga sama da 8,000, sun kama mutum 11,600, tare da ƙwato makamai fiye da 10,000.

Ya tabbatar da cewa ƙoƙarin da ake yi yana sa hanyoyi na ƙara zama lafiya.

Ya ƙara da cewa, “Ko da yake har yanzu muna da aiki a gaba, hanyoyin mu sun fara zama mafi aminci.

“Hanyar Abuja zuwa Kaduna, wadda aka fi sani da rashin tsaro, tana daga cikin misalan da ke nuna irin cigaban da muke samu.

“Kamar yadda na faɗa, har yanzu akwai aiki da yawa a gaba, kuma ba za mu yi ƙasa a gwiwa ba.

“Haka kuma, sama da mutum 8,000 da aka sace an kuɓutar da su cikin nasara.

“Za mu ci gaba da ƙoƙarin rage yawan waɗanda ake sacewa tare da bunƙasa nasarorin mu wajen hana laifuka, gano masu ma’aikatan su, da kuma hukunta su.”

Idris ya ƙara da cewa, bayan da Kotun Tarayya ta ayyana ƙungiyar Lakurawa a matsayin ’yan ta’adda, jami’an tsaro sun samu cikakken ikon amfani da ƙarfin da ya dace wajen murƙushe su.

Dangane da tattalin arziki, Ministan ya bayyana cewa sauye-sauyen da gwamnati ke aiwatarwa suna samar da ingantaccen sakamako, musamman cire tallafin fetur wanda ya hana asarar ɗaruruwan biliyoyin naira a kowace shekara.”

Ya jaddada cewa shigar da tsarin Electronic Foreign Exchange Matching System (EFEMS) a watan Disamba na 2023 ya inganta gaskiya a harkar canjin kuɗi, inda ya taimaka wajen warware bashin dalar Amurka da aka tara tun baya, da kuma dawo da ƙwarin gwiwar masu zuba jari.

“Makon jiya, Naira ta kai matsayi mafi ƙarfi cikin watanni takwas a kasuwar canji ta hukuma, yayin da jarin da ƙasashen waje ke zubawa a Kasuwar Hannun Jari ta Nijeriya ya ƙaru daga kashi 4 a tsakiyar 2023 zuwa kashi 16 a ƙarshen 2024.”

Ministan ya kuma bayyana cewa a shekarar 2024, Nijeriya ta zama ƙasa mafi jan hankalin masu zuba jari a ɓangaren man fetur da iskar gas a nahiyar Afrika, inda aka samu sama da dala biliyan 5.

Idris ya bayyana shekarar 2025 a matsayin shekara ta cigaba da gina nasarorin da aka samu a cikin wa’adin farko na mulkin Tinubu.

Ya ce za a gudanar da tarukan ministoci a duk mako na tsawon watanni uku masu zuwa domin tattauna nasarorin da aka samu a fannoni daban-daban.

Ya ce: “A cikin watanni uku masu zuwa, yayin da muke gab da cika shekaru biyu na mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, za mu kawo ministoci zuwa wannan dandali a kowanne mako.

“Shekarar 2025 ita ce shekara ta ƙarfafa nasarorin da muka samu a cikin watanni 19 na farko na wannan gwamnati.

“Wannan zaman farko na 2025 dama ce ta tunatar da mu waɗannan nasarori da kuma tabbatar da irin cigaban da ake samu yayin da muke shirin shiga rabin wa’adin mulkin nan.”

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Sin Ta Ayyana Matakan Bunkasa Harkokin Sayayya Da Zuba Jarin Waje

Next Post

Waɗanda Suka Sace Jigo A Jam’iyyar APC Sun Buƙaci A Biya Su Naira Miliyan 350

Related

Gwamna Dikko Zai Sake Tsarin Babbar Kasuwar Jihar Katsina
Manyan Labarai

Jami’an Tsaron Katsina Sama Da 100 Sun Rasu A Yaƙi Da ‘Yan Ta’adda – Gwamnati

2 hours ago
Tinubu Ya Karrama Mata ‘Yan Ƙwallon Nijeriya Da Lambar Girmamawa (OON), Dala Dubu 100 Da Gidaje
Da ɗumi-ɗuminsa

Tinubu Ya Karrama Mata ‘Yan Ƙwallon Nijeriya Da Lambar Girmamawa (OON), Dala Dubu 100 Da Gidaje

14 hours ago
Kakakin Majalisar Wakilai, Abbas, Ya Yi Jimamin Rasuwar Buhari, Ya Ce Mutuwa Ce Da Ta Girgiza Shi
Da ɗumi-ɗuminsa

SDP: Fadar Shugaban Ƙasa Ta Yi Wa El-Rufai Shaguɓe Da Ayyana Shi A Matsayin Ɗan Gudun Hijirar Siyasa

16 hours ago
Sojoji, DSS Sun Hallaka Ƴan Bindiga 45 A Neja
Manyan Labarai

Sojoji, DSS Sun Hallaka Ƴan Bindiga 45 A Neja

18 hours ago
Harin Sojojin Sama Ya Hallaka Manyan Shugabannin ISWAP A Borno
Manyan Labarai

Harin Sojojin Sama Ya Hallaka Manyan Shugabannin ISWAP A Borno

20 hours ago
Shetima Zai Wakilci Nijeriya A Taron Tsarin Abinci A Addis Ababa
Manyan Labarai

Shetima Zai Wakilci Nijeriya A Taron Tsarin Abinci A Addis Ababa

2 days ago
Next Post
Waɗanda Suka Sace Jigo A Jam’iyyar APC Sun Buƙaci A Biya Su Naira Miliyan 350

Waɗanda Suka Sace Jigo A Jam'iyyar APC Sun Buƙaci A Biya Su Naira Miliyan 350

LABARAI MASU NASABA

EFCC Ta Kama Mutane 11 Kan Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Akwa Ibom

EFCC Ta Kama Mutane 11 Kan Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Akwa Ibom

July 29, 2025
Gwamna Dikko Zai Sake Tsarin Babbar Kasuwar Jihar Katsina

Jami’an Tsaron Katsina Sama Da 100 Sun Rasu A Yaƙi Da ‘Yan Ta’adda – Gwamnati

July 29, 2025
An Gudanar Da Taron Dandalin Tattaunawar Neman Sabon Tunani Na Asali Na 2025

An Gudanar Da Taron Dandalin Tattaunawar Neman Sabon Tunani Na Asali Na 2025

July 28, 2025
Ambaliyar Ruwa: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Ya Ƙaru Zuwa 23 A Jihar Adamawa

Ambaliyar Ruwa: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Ya Ƙaru Zuwa 23 A Jihar Adamawa

July 28, 2025
Sin: Ya Kamata A Warware Sabanin Tattalin Arziki Da Cinikayya Ta Hanyar Tattaunawa

Sin: Ya Kamata A Warware Sabanin Tattalin Arziki Da Cinikayya Ta Hanyar Tattaunawa

July 28, 2025
Kotun Ta Ci Tarar Hukumar NYSC Kan Haramtawa ‘Yan Bautar Ƙasa Mata Sanya Siket Da Tauye Musu ‘Yanci

Kotun Ta Ci Tarar Hukumar NYSC Kan Haramtawa ‘Yan Bautar Ƙasa Mata Sanya Siket Da Tauye Musu ‘Yanci

July 28, 2025
An Fara Sabon Zagayen Tattaunawar Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka A Sweden

An Fara Sabon Zagayen Tattaunawar Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka A Sweden

July 28, 2025
Sin Ta Samu Iska Mai Ni’ima Da Ruwa Mai Inganci A Rabin Farko Na Bana

Sin Ta Samu Iska Mai Ni’ima Da Ruwa Mai Inganci A Rabin Farko Na Bana

July 28, 2025
Sin Za Ta Ba Da Tallafin Kula Da Yara A Fadin Kasar

Sin Za Ta Ba Da Tallafin Kula Da Yara A Fadin Kasar

July 28, 2025
Tinubu Ya Karrama Mata ‘Yan Ƙwallon Nijeriya Da Lambar Girmamawa (OON), Dala Dubu 100 Da Gidaje

Tinubu Ya Karrama Mata ‘Yan Ƙwallon Nijeriya Da Lambar Girmamawa (OON), Dala Dubu 100 Da Gidaje

July 28, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.