Karamar ministar ma’aikatar harkokin ‘yansanda, Hajia Imaan Sulaiman-Ibrahim, ta ce nan ba da dadewa ba gwamnatin tarayya za ta fara janye jami’an ‘yansanda da ke bada kariya ga Hamshakai (VIPs) za ta kuma bullo da sabbin dabarun aikin ‘yansanda.
Ta bayyana hakan ne a wani taron kwana biyu da aka shirya wa manyan daraktocin ma’aikatar hukumar aikin ‘yansanda.
Ministar ta ce, muhimman ayyukan ma’aikatar su ne ingantawa da aiwatar da rahoton garambawul na aikin ‘yansanda, gyara dokar ‘yansanda, aiwatar da umarnin shugaban kasa kan janye jami’ai daga (VIPs) da sauransu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp