Ministan albarkatun ruwa da tsaftar mahalli, Farfesa Joseph Utsev, a ranar Laraba, ya nanata kudirin gwamnatin tarayya na magance kalubalen zamantakewa da tattalin arzikin kasar nan na dindindin.
Da yake jawabi a wani taron karawa juna sani a shiyyar Kudu-maso-Kudu kan Kafawa tare da karfafa kungiyoyin masu ruwa da tsaki a harkar noman rani a Nijeriya da aka gudanar a otal din Warbridge dake Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom, ministan ya jaddada muhimmancin albarkatun ruwa, yana mai ba da tabbacin cewa, gwamnatin tarayya na kokarin ganin ta magance kalubalen abinci a kasar nan.
Ministan wanda ya samu wakilcin babban sakatare, Mista Richard Pheelangwah, ya ce: “Kamar yadda ku ka sani, gwamnati mai ci a karkashin jagorancin shugaban kasa, Bola Tinubu, ta kafa dokar ta-baci kan samar da abinci ta hanyar noman rani.
“Ina matukar farin cikin sanar da ku cewa, ma’aikatar albarkatun ruwa da tsaftar muhalli ta tarayya, a wani bangare na alkawurran da ta dauka, ta bayyana bangaren noman rani a matsayin daya daga cikin muhimman manufofinta na yin daidai da kokarin da gwamnatin tarayya ke yi na fitar da ‘yan Nijeriya miliyan 100 daga kangin talauci nan da shekarar 2030.”