• English
  • Business News
Wednesday, October 29, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnati Ta Fara Binciken Ministar Jin ƙai Kan Umarnin Zuba Miliyan N585 A Asusun Ma’aikaciya – Minista

by Sulaiman
2 years ago
Yajin aiki

Sakamakon ƙorafe-ƙorafe da rahotannin zargin da ake yi wa Ministar Harkokin Agaji da Jinƙai, Dakta Betta Edu, Gwamnatin Tarayya ta fara binciken yadda aka zuba naira miliyan N585.2 a asusun ajiyar wata ma’aikaciyar gwamnati, bisa umarnin ita ministar.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana haka a ranar Lahadi cikin wata sanarwa ga manema labarai.

  • Matatar Ɗangote Ta Karɓi Jirgi Na Biyar Na Ɗanyen Mai
  • Tinubu Ya Bada Umarnin Binciken Ma’aikatar Jin Kai Kan Zargin Karkatar Da Miliyan N585

Ita dai Minista Betta Edu, ta na ci gaba da shan ragargaza daga ko’ina a faɗin ƙasar nan bayan an fallasa yadda ta bada umarnin a zuba zunzurutun kuɗi har naira miliyan N585.2 a cikin asusun banki na wata ma’aikaciyar gwamnati, wadda ita ce akawu mai kula da Kuɗaɗen Tallafin Marasa Galihu a ma’aikatar.

Dakta Edu ta fitar da wasiƙar bada umarnin zuba wa ma’aikaciyar kuɗin ne ga Akanta Janar na Tarayya a cikin Disamba, 2023, inda ta rubuta cewa a zuba kuɗin cikin asusun, duk da cewa yin hakan ya karya doka.

Duk da cewa Akanta Janar ya ce mata yin hakan karya doka ne, amma ya amince an biya kuɗin cikin aljihun asusun ma’aikaciyar, wanda ministar ta ce a zuba mata kuɗin.

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Tarayya Ta Saki Naira Biliyan 2.3 Ga ASUU

Sulhu Da ’Yan Bindiga Ba Tare Da Sun Ajiye Makamai Ba Tamkar Miƙa Wuya Ne – Gwamna Lawal ga Hukumomin Tsaro

Wannan ne ya jawo ce-ce-ku-ce da nuna damuwar da har Gwamnatin Tarayya ta gaggauta fara bincike.

Sai dai ita kuma Edu ta ce ba ta aikata wani laifi da ya saɓa wa doka ba, duk kuwa da cewa akwai tambayoyin da ma’aikatar ta ya kamata ta amsa, haka shi ma ofishin Akanta Janar ɗin akwai tambayoyin da ya kamata ya amsa domin warware zare da abawa.

Cikin sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi, Idris ya ce yanzu haka gwamnati ta fara bincike, sannan kuma ta gamsu da yadda ‘yan Nijeriya su ka nuna damuwarsu dangane da wannan zargi da ake yi wa ita ministar.

Ya ci gaba da cewa, Gwamnatin Tarayya, a ƙarƙashin shugabancin Bola Tinubu, ba ta gudanar da ayyukan ta cikin ƙumbiya-ƙumbiya.

Ya ce gwamnatin za ta tura kuɗaɗe a inda ya dace kai-tsaye, domin ayyukan biyan buƙatun ‘yan Nijeriya.

Haka nan kuma Idris ya yi kira tare da bada shawara ga jama’a da cewa a maida hankali wajen samun sahihan bayanai daga Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai da ya ke jagoranta.

Hakan a cewar sanarwar sa, ya na da nasaba da ganin yadda ake ta yaɗa labarai da bayanai marasa tushe balle makama da su ka shafi Gwamnatin Tarayya.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Asuu
Labarai

Gwamnatin Tarayya Ta Saki Naira Biliyan 2.3 Ga ASUU

October 29, 2025
Sulhu Da ’Yan Bindiga Ba Tare Da Sun Ajiye Makamai Ba Tamkar Miƙa Wuya Ne – Gwamna Lawal ga Hukumomin Tsaro
Labarai

Sulhu Da ’Yan Bindiga Ba Tare Da Sun Ajiye Makamai Ba Tamkar Miƙa Wuya Ne – Gwamna Lawal ga Hukumomin Tsaro

October 29, 2025
majalisar kasa
Labarai

Majalisar Wakilai Ta Amince Da Bukatar Amso Bashin Dala Biliyan 2.34 A Kasuwar Jari Ta Duniya

October 29, 2025
Next Post
Equatorial Guinea

Equatorial Guinea Za Ta Daukaka Huldarta Da Sin Zuwa Wani Sabon Matsayi, In Ji Shugaban Kasar

LABARAI MASU NASABA

Asuu

Gwamnatin Tarayya Ta Saki Naira Biliyan 2.3 Ga ASUU

October 29, 2025
Sabon Ingantaccen Hadin Gwiwar “Sin-ASEAN 3.0″ Ya Kafa Sabon Misali Na Hadin Kan Yanki

Sabon Ingantaccen Hadin Gwiwar “Sin-ASEAN 3.0″ Ya Kafa Sabon Misali Na Hadin Kan Yanki

October 29, 2025
Sulhu Da ’Yan Bindiga Ba Tare Da Sun Ajiye Makamai Ba Tamkar Miƙa Wuya Ne – Gwamna Lawal ga Hukumomin Tsaro

Sulhu Da ’Yan Bindiga Ba Tare Da Sun Ajiye Makamai Ba Tamkar Miƙa Wuya Ne – Gwamna Lawal ga Hukumomin Tsaro

October 29, 2025
An Yi Taron Tataunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Moscow, Manama, Da Budapest

An Yi Taron Tataunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Moscow, Manama, Da Budapest

October 29, 2025
majalisar kasa

Majalisar Wakilai Ta Amince Da Bukatar Amso Bashin Dala Biliyan 2.34 A Kasuwar Jari Ta Duniya

October 29, 2025
An Samu Ingantuwar Yanayin Iska Da Ruwa Cikin Watanni 9 Na Farkon Bana A Sin

An Samu Ingantuwar Yanayin Iska Da Ruwa Cikin Watanni 9 Na Farkon Bana A Sin

October 29, 2025
Kotu Ta Umarci Ƙwace Dala 49,700 Daga Tsohon Jami’in INEC

Kotu Ta Umarci Ƙwace Dala 49,700 Daga Tsohon Jami’in INEC

October 29, 2025
Yadda Kasar Sin Ke Kara Kyautata Tsarin Kare Muradun Al’umma A Bangaren Shari’a

Yadda Kasar Sin Ke Kara Kyautata Tsarin Kare Muradun Al’umma A Bangaren Shari’a

October 29, 2025
COAS Shaibu Ya Sha Alwashin Murƙushe ‘Yan Ta’addar Lakurawa 

COAS Shaibu Ya Sha Alwashin Murƙushe ‘Yan Ta’addar Lakurawa 

October 29, 2025
Binciken ‘Yan Sanda Kan Wanda Ake Zargi Da Tawayen “‘Yancin Kan Taiwan” Mataki Ne Na Adalci Don Kare Hadin Kan Kasa

Binciken ‘Yan Sanda Kan Wanda Ake Zargi Da Tawayen “‘Yancin Kan Taiwan” Mataki Ne Na Adalci Don Kare Hadin Kan Kasa

October 29, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.