Dan gwagwarmayar siyasa kuma tsohon mataimakin sakataren watsa labarai na jam’iyyar APC na kasa, Kwamared Timi Frank, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta yin da bincike kan yunkurin ‘Yan Boko Haram na kaiwa dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, hari.
Frank ya kuma kirayi gwamnatin da ta tabbatar da sanya tsaro mai inganci a kusa da tsohon mataimakin shugaban kasar, ya kuma bukaci kasashen waje da su sanya idanu kan wannan lamarin.
- Atiku Ya Soki Shirin Tinubu Na Bai Wa ‘Yan Nijeriya Tallafin ₦8000
- Yadda Fintiri Da Atiku Suka Gudanar Da Bikin Sallah A Adamawa
Dan gwagwarmayar siyasan ya shaida cewa wasu da ake zargin mambobin kungiyar Boko Haram ne sun yi yunkurin hallaka Atiku Abubakar a gidansa da ke Yola ta jihar Adamawa a ranar Lahadi.
A sanarwar manema labarai da ya fitar a ranar Litinin a Abuja, Timi Frank, ya ce, wani da aka kama ake zargi ya tabbatar wa ‘yansanda wani yunkurin tayar da bama-bamai a babban masallacin Juma’a ta Modibbo Adama, gidan Atiku Abubakar da jami’ar American University of Nigeria, da ke cikin garin Yola.
Ya ce: “Bayanan tsaro ya zo mana da safiyar yau cewa wasu mambobin kungiyar Boko Haram su 4 da suka fito tun daga Danboa da ke jihar Borno wajajen karfe 9:45 na daren Lahadi zuwa gidan Atiku Abubakar da ke Yola domin aiwatar da shirinsu da manufarsu.
Ya ce, akwai bukatar gwamnatin tarayya ta tashi tsaye wajen kaddamar da bincike tare da dakile faruwar hakan a nan gaba da samar da kariya ga Atiku Abubakar.