Gwamnatin Jihar Kaduna karkashin jagorancin Gwamna Uba Sani, ta dage dokar hana fita a Kaduna da Zariya, wadda ta sanya daga karfe 6 na yamma zuwa 8 na safe.
Wannan mataki ya biyo bayan nazarin yanayin tsaro da aka samu a yankunan.
- Yadda Mahara Suka Jefa Bam A Ofishin Jami’yyar APP A Ribas
- Kwanaki 11 Da Hawa Kujerar Mulki, Mataimakin Shugaban Iran Ya Yi Murabus
Yanzu haka, jama’a za su iya zirga-zirga kuma su gudanar da harkokinsu na yau da kullum ba tare da takura ba.
Amma dai, gwamnati ta jaddada cewa dole ne a nemi izini daga hukumomi kafin gudanar da taro domin kaucewa rikici.
Hukumomin tsaro za su ci gaba da sanya ido tare da daukar matakai kan duk wanda ya kawo cikas ga zaman lafiya a jihar.
Gwamna Sani, ya yaba da kokarin hukumomin tsaro, shugabannin addinai da na gargajiya, da sauran masu ruwa da tsaki wajen tabbatar da zaman lafiya yayin zanga-zangar #EndBadGovernance a Kaduna da Zariya.
Ya kuma tabbatar musu da cewa zai ci gaba da yin aiki tare da su domin tabbatar da zaman lafiya, hadin kai, da ci gaban Jihar Kaduna.