Babban lauyan gwamnatin tarayya, kuma ministan shari’a, Abubakar Malami, SAN, ya janye tuhumar cin hanci da rashawa na Naira biliyan 1.84 da ake tuhumar Nicholas Ashinze, tsohon mataimakin mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Sambo Dasuki, da wasu takwas.
Malami ya janye karar ne a babbar kotun tarayya da ke Abuja, bayan da ya karbi shari’ar a hannun hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC.
Lauyan da ya wakilci ministan a kotun, David Kaswe, bai bayyana dalilin janye karar ba.
A baya dai, Hukumar EFCC ta kira shaidu bakwai a shari’ar da aka fara tun shekaru biyar da suka gabata. Hukumar ta shira kan ci gaba da sauraron karar yayin da lauya daga ofishin AGF Malami, Mista Kaswe, ya sanar da karbar karar daga hannun lauyan hukumar EFCC.
Lauyan EFCC, Offem Uket, ya ce bai san cewa ofishin AGF ya karbi ragamar ci gaba da sauraron karar ba, amma duk da haka, lauyan bai yi musun janye wa ya maida karar zuwa ga lauya mai wakiltar ofishin babban lauyan gwamnati kuma ministan shari’a ba.