Gwamnatin tarayya ta kammala cikakken tsarin manhajar koyarwa na makarantun bai daya da suka shafi na babbar Sakandare da kuma ilimin fasaha, wadanda aka yi da zummar samar da hanyoyin da za su bunkasa lamarin koyon karatu da irin sakamakon da za a samu.
Da take bayyana irin ci gaban da aka samu a madadin Ministan ilimi karamar Ministan, Dakta. Maruf Tunji Alausa, karamar Minisatar ilimi Farfesa Suwaiba Sai’d Ahmad, ta ce sake yadda manhajar da aka yi tare da tuntubar hukumomin bincike da bunkasa ilimi(NERDC),ilimi bai daya UBEC shirya Jarabawar kammala Sakandare, NSSEC, kula da ilimin fasaha NBTE sai kuma sauran masu ruwa da tsaki.
- Gwamnatin Kogi Ta Jaddada Aniyar Magance Ambaliya Da Zaizayar Ƙasa
- Mun Tara Kuɗi Sama Da Naira Miliyan 170 Na Fatun Layya – Sheikh Bala Lau
Kamar yadda ta bayyana,sabon tsarin ilimi ta banagaren samar da daidaito ta bangaren darussan da za’ayi da fahimatar lamarin a bayyane zai fara aiki ne a shekarar karatu ta 2025/26.
A jawabin ‘yan jaridu wanda darekta na bangaren manema labarai da al’amuran da suka shafi jama’a na ma’aikatar ilimi ta tarayya Folasade Boriowo, abin ya bayyana; “A sashen Firamare , ‘yan aji 1- 3 za su byi darussa 9–10, su kuma wadanda suke aji 4–6 zasu yi darussa 10–12.Sai bagaren karamar Sakandare, abin ya fara ne daga darussa 12–14; Babbar Sakandare kuma dalibanta za su yi darussa 8–9; yayin da su kuma fannin fasaha za su yi darussa 9–11.”
Ahmad ya bayyana manhajar an tsara ta ne saboda an rage abubuwan da ta kunsa, aka kara maida hankali ga koyo domin tabbatar da cewa lamarin da ya shafi ilimi ya ci gaba da zama yana tafiya daidai zamanin da ake ciki yanzu a fadin duniya gaba daya.
Ma’aikatar ta jinjinawa masu ruwa da tsaki akan irin maida hankalin da suka yi, aka kuma kara jaddada cewa shi lamarin sabon tsarin darussa za’a tabbatar da an bi shi kamar yadda yadda yake, da kuma tabbatar da an yi amfani da shi a fadin tarayyar Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp