Dangane da karuwar haɗurran motocin dakon kaya da tankar man fetur a manyan tituna, gwamnatin tarayya ta kafa wani kwamiti na musamman da zai binciki matsalar tare da samar da hanyoyin magance matsalolin cikin gaggawa.
Kwamitin ya kunshi wakilan kungiyar ma’aikatan sufurin ta Nijeriya (RTEAN), hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC), cibiyar fasahar sufuri ta Nijeriya (NITT), jami’an tsaron Nijeriya na farin kaya (NSCDC), kungiyar masu motocin haya ta kasa (NARTO).
- Makiyayi Ya Kashe Abokai 2 A Nasarawa Kan Rikicin Kiwo
- Akwai Ƙarin Gishiri A Yawan Masu Sauyin Jam’iyya Zuwa APC – El-Rufai
Sauran mambobin kwamitin sun hada da wakilan kungiyar ma’aikatan sufurin mota ta kasa (NURTW), kungiyar makarantar tuki ta Nijeriya (DSAN), kungiyar direbobi mata (FDA), kungiyar masu motocin dakon kayayyakin da ake shigo da su ta ruwa (AMATO) da kuma mambobin kungiyar masu binciken tuki ta Nijeriya (IDIN).
Da yake jawabi a wajen kaddamar da kwamitin, Ministan Sufuri, Sanata Said Alkali, ya jaddada muhimmancin shawo kan kalubalen hadurran da ke ci gaba da barazana da haddasa munanan asarar rayuka da dukiyoyi.
Alkali wanda ya jaddada bukatar a gaggauta kawo karshen wannan mumunan lamari, ya bai wa kwamitin mako guda ya gabatar da rahotonsa, inda ya jaddada cewa, tsaro da inganci su ne kan gaba a cikin manufofin gwamnatin Bola Tinubu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp