Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya kafa wani kwamitin ministoci goma da zai jagoranci shirye-shiryen jana’izar marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, wanda ya rasu a birnin London ranar Lahadi, 13 ga Yuli, 2025, bayan doguwar jinya.
Sanarwar da ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya ya fitar ranar Litinin ta bayyana cewa Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, ne zai jagoranci kwamitin. Za a gudanar da jana’izar a Daura, jihar Katsina, inda ake jiran isowar gawar marigayin daga Ingila.
- Sharrin Ƴan Adawa Ne, Gwamnati Ta Ƙaryata Labarin Cire SGF AkumeÂ
- Neja: Cikin Wata 10 Ibtila’i Ya Lakume Rayuka Sama Da 400 – NSMA
Mambobin kwamitin sun haɗa da ministoci daga ɓangarori daban-daban ciki har da harkokin kuɗi, tsaro, yaɗa labarai, ayyuka, gidaje da al’adu, da kuma masu ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, siyasa da tsare-tsare. Haka kuma, an haɗa da babban sufeto janar na Ƴansanda da shugaban hukumar DSS da shugaban ma’aikatan tsaro.
Shugaba Tinubu ya kuma umurci dukkanin ma’aikatun gwamnatin tarayya da su ajiye rijistar karɓar gaisuwa domin bai wa ƴan Nijeriya da sauran wakilan ƙasashen waje damar bayyana ta’aziyyarsu. Ma’aikatar Harkokin Waje za ta karɓi gaisuwa daga ofisoshin diplomasiyya da jakadun ƙasashen duniya.
An riga an aika da tawagar da ta ƙunshi Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa domin dawo da gawar Buhari zuwa gida. A halin yanzu, tutar Nijeriya na ci gaba da zama a ƙasa a dukkan ofisoshin gwamnati domin girmamawa da jimamin rasuwar tsohon shugaban ƙasar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp