Gwamnatin Tarayya ta roƙi Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Nijeriya (ASUU) da ta soke shirin tana fara yajin aiki, inda ta tabbatar da cewa za ta dukkanin buƙatun da ƙungiyar ta gabatar.
Ministan Ilimi, Dakta Maruf Olatunji Alausa, ne ya yi wannan roƙo a Abuja ranar Laraba yayin da yake wa manema labarai bayani game da ci gaban da aka samu tsakanin gwamnati da ƙungiyoyin jami’o’i.
- Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung
- Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci
Ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya ba da umarni cewa a yi duk mai yiwuwa don kaucewa sake dakatar da karatu a jami’o’i.
Alausa ya ce an sake kafa Kwamitin Tattaunawa na Mahmud Yayale Ahmed domin hanzarta tattaunawa da ƙungiyoyin malamai da na ma’aikatan jami’o’i, kwalejoji.
Ya ce mafi yawan buƙatun ƙungiyoyin an riga an fara magance su, ciki har da sakin naira biliyan 50 na alawus ɗin malamai da kuma naira biliyan 150 da aka saka a kasafin kuɗin 2025 don farfaɗo da jami’o’i da sauran manyan makarantu.
“Yanzu muna kammala sabbin sharuɗan aikin da ASUU ta gabatar, kuma za mu bayyana amsar gwamnati nan ba da jimawa ba,” in ji shi.
“Shugaba Tinubu yana da niyyar kawo ƙarshen wannan matsala gaba ɗaya.”
Ya roƙi ASUU da ta ci gaba da tattaunawa maimakon fara yajin aiki, yana mai tabbatar da cewa gwamnati na da niyyar gaskiya da jajircewa wajen warware matsalar.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa ASUU ta fara shirin tursasa wa mambobinta fara yajin aikin gargadi, yayin da wa’adin kwanaki 14 da ta bai wa gwamnati zai ƙare a ranar Lahadi mai zuwa.