Karamin Ministan Tsaro kuma tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle ya bayyana cewar gwamnatin tarayya ta shirya yaki da ‘yan bindiga a duk inda suke.
‘’Akwai kayyayaki na yaki sosai kuma muna ba da tabbaci cewa, idan Allah ya yadda za a ga sakamako mai kyau.
- Mahara Sun Sace Sarki Da Fadawansa A Garin Pupule Na Jihar Taraba
- Manyan Hafsoshin Sojan Nijeriya Sama Da 113 Sun Yi Ritaya Daga Aikin Soja
“Kuma za a rika tunkarar su duk inda suke, duk dajin da suke a kai musu farmaki ba tare da cewa sai an jira sun taho sun yaki al’umma ba’’, in ji shi.
Ministan, ya ce akwai alaka tsakanin jami’in tsaro sai dai matsalar da su ke fama da ita a wannan yaki da ta’adanci ita ce ta ‘’masu ba da sirrin jami’an tsaro wanda su ne babban matsalar,’’ a cewarsa.
Matawalle dai ya jadadda cewa, an dauki kwararan matakan kiyaye sake afkuwar irin iftila’in da ya faru a Kauyen Tudun Biri da ke Jihar Kaduna.
Ya ce shugaba Bola Tinubu ya umurce su da a ‘’tabbatar da adalci da kuma tabbatuwa cewa matakin da za a dauka za a ga karshen irin wadannan matsaloli’’, kuma ‘‘gwamnati ta dauki mataki kwakwara a kan wannan abu’’.
Ya ce ta’aziyar da jami’in gwamanati suka kai wa wadanda iftila’in ya shafa da sadaukar da albashinsu ‘‘domin tabbatar wa duniya cewa wannan abu da ya faru, ba wanda ya ji dadinsa’’.
Kazalika, ya kuma sha alwashin cewa ‘’wannan abu ba zai sake faruwa ba’’ saboda an ‘’dauki mataki kwakkwara a kan wannan, kuma za a sanar da ‘yan Nijeriya abin da ake ciki’’.