• English
  • Business News
Tuesday, October 28, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnati Ta Umarci Mayar Da Waɗanda Fashewar Tankar Mai Ta Shafa A Suleja Zuwa Manyan Asibitoci

by Sulaiman
9 months ago
Fashewar tankar mai

Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin gaggawa na tura mutanen da suka jikkata a hatsarin fashewar tankar man fetur da ya faru a Suleja, Jihar Neja, daga Asibitin Suleja zuwa manyan asibitoci domin samun ingantacciyar kulawar lafiya cikin sauri.

 

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan yayin wata ziyara da ya kai Suleja a ranar Lahadi.

  • Tinubu Ya Himmatu Wajen Kammala Titin Abuja Zuwa Kano Cikin Watanni 14 – Minista
  • TikTok Ya Dawo Aiki A Amurka Bayan Matakin Da Trump Ya Ɗauka 

Idris ya jagoranci wata tawaga daga Gwamnatin Tarayya, ciki har da Ministan Harkokin Jinƙai da Rage Talauci, Dr. Nentawe Yilwatda, domin tantance halin da ake ciki da kuma miƙa ta’aziyyarsu ga Gwamnatin Jihar Neja da mazauna yankin bisa hatsarin da ya faru a Dikko Junction.

 

LABARAI MASU NASABA

Tsohon Kwamishina Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Sayar Da Filin Makaranta Kan Miliyan 100

An Matsa Min Sai Na Koma Jam’iyyar APC – Gwamnan Filato

“Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu yana cikin matuƙar jimami kan wannan mummunan al’amari. Ya umurce mu da mu zo nan don ganin halin da ake ciki. Mun zagaya ɗakin masu jinya, kuma mun ga waɗanda ke cikin mummunan hali. Muna nan ana duba su, amma abin takaici, ɗaya daga cikinsu ya rasu. Wannan shi ne mutum na takwas da ya rasu sakamakon wannan hatsari. Gwamnatin Tarayya za ta tabbatar da cewa an yi gaggawar tura waɗannan mutanen da suka jikkata zuwa manyan asibitoci,” inji Idris.

 

Ministan ya yaba da gaggawar Gwamnatin Jihar Neja wajen bayar da taimakon gaggawa ga waɗanda suka jikkata.

 

Yayin da yake bayyana damuwarsa kan yawaitar fashewar tankar man fetur a ƙasar, inda mutane sama da 265 suka rasa rayukansu a cikin watanni biyar, Idris ya bayyana cewa Shugaban Ƙasa Tinubu ya kafa kwamiti domin bincikar musabbabin faruwar waɗannan al’amura da kuma samar da mafita don hana faruwar hakan a gaba.

 

“Shugaban ƙasa yana cikin damuwa sosai game da abin da ya faru. Ya kafa kwamitin bincike na musamman don gano musabbabin waɗannan abubuwan. A cikin watanni biyar da suka gabata, mun fuskanci manyan haɗura huɗu: ɗaya tsakanin Ibadan da Ife, wani a Agaie, Jihar Neja, inda mutane 48 suka rasa rayukansu, wani kuma a Jihar Jigawa inda mutane 144 suka mutu, sannan wannan a Suleja inda kusan mutane 80 suka mutu. Idan aka haɗa yawan waɗanda suka rasa rayukansu, sama da mutane 265 ne suka mutu a irin waɗannan haɗurra.

 

“Kwamitin da aka kafa, wanda ya ƙunshi manyan ma’aikatu da hukumomi kamar Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, NEMA, FRSC, NUPRC, da NARTO, zai binciki musabbabin haɗurran tare da bayar da shawarwari don hana sake faruwar su,” inji Idris.

 

Ministan ya ce, a bisa umarnin da Shugaban Ƙasa ya bayar kwanan nan, Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Ƙasa (NOA) za ta ƙara himma wajen wayar da kan jama’a kan haɗarin kwasan man fetur daga tankokin mai da suka yi hatsari domin hana aukuwar irin waɗannan al’amura nan gaba. Ya yi tir da wannan ɗabi’a, yana mai bayyana ta a matsayin abin da ba za a yarda da shi ba.

 

Tawagar ta fara kai ziyara ta jaje ga Sarkin Suleja, Alhaji Auwal Ibrahim, sannan ta ziyarci waɗanda suka jikkata a Asibitin Suleja da wurin da haɗarin ya faru.

 

Sauran waɗanda suka kasance a tawagar har da Daraktocin Janar na Gidan Talabijin na Nijeriya (NTA), Abdulhamid Dembos; Muryar Nijeriya (VON), Jibrin Baba Ndace; da Rediyon Tarayya na Nijeriya (FRCN), Mohammed Bulama.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tsohon Kwamishina Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Sayar Da Filin Makaranta Kan Miliyan 100
Labarai

Tsohon Kwamishina Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Sayar Da Filin Makaranta Kan Miliyan 100

October 28, 2025
An Matsa Min Sai Na Koma Jam’iyyar APC – Gwamnan Filato
Manyan Labarai

An Matsa Min Sai Na Koma Jam’iyyar APC – Gwamnan Filato

October 28, 2025
’Yansanda Sun Ƙaryata Rahoton Ƙone Gidan Shugaban Jam’iyyar PDP A Bauchi
Labarai

’Yansanda Sun Ƙaryata Rahoton Ƙone Gidan Shugaban Jam’iyyar PDP A Bauchi

October 28, 2025
Next Post
Bidiyon Rashin Ɗa’a: Hukumar Tace Fina-finai Ta Dakatar Da Soja-boy Daga Shiga Duk Wata Harka Ta Kannywood

Bidiyon Rashin Ɗa'a: Hukumar Tace Fina-finai Ta Dakatar Da Soja-boy Daga Shiga Duk Wata Harka Ta Kannywood

LABARAI MASU NASABA

Tsohon Kwamishina Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Sayar Da Filin Makaranta Kan Miliyan 100

Tsohon Kwamishina Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Sayar Da Filin Makaranta Kan Miliyan 100

October 28, 2025
An Matsa Min Sai Na Koma Jam’iyyar APC – Gwamnan Filato

An Matsa Min Sai Na Koma Jam’iyyar APC – Gwamnan Filato

October 28, 2025
’Yansanda Sun Ƙaryata Rahoton Ƙone Gidan Shugaban Jam’iyyar PDP A Bauchi

’Yansanda Sun Ƙaryata Rahoton Ƙone Gidan Shugaban Jam’iyyar PDP A Bauchi

October 28, 2025
Mutum 18 Sun Mutu, 40 Sun Jikkata A Hatsarin Mota A Kebbi 

An Kashe Mutum 10 A Harin Ramuwar Gayya A Jihar Kebbi

October 28, 2025
Ganduje Na Kara Shan Matsin Lamba A Kan Ya Sauka

Zargin Almundahana: An Ɗage Shari’ar  Ganduje Da Matarsa Saboda Rashin Miƙa Takardu

October 28, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

Sojoji Sun Kashe Masu Yi Wa ISWAP 4 Safarar Makamai A Borno

October 28, 2025
Fashewar tankar mai

APC Ta Yi Barazanar Dakatar Duk Kwamishinan Da Bai Sanya Irin Hular Tinubu Ba

October 27, 2025
An Yi Taron Tattaunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Amurka

An Yi Taron Tattaunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Amurka

October 27, 2025
Wakilan Sin Da Na Amurka Sun Yi Tattaunawa Mai Ma’ana Da Zurfi Da Kuma Amfani

Wakilan Sin Da Na Amurka Sun Yi Tattaunawa Mai Ma’ana Da Zurfi Da Kuma Amfani

October 27, 2025
Ribar Manyan Masana’antun Kasar Sin Ta Karu Da Kashi 3.2 Cikin Dari A Watanni Tara Na Farkon Bana

Ribar Manyan Masana’antun Kasar Sin Ta Karu Da Kashi 3.2 Cikin Dari A Watanni Tara Na Farkon Bana

October 27, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.