Gwamnatin tarayya ta bai wa kamfanin gina hanyoyi na ‘Infiouest Construction Company’ wa’adin watanni 14 da ya tabbatar ya kammala rukunin aiki na biyu na titin naira biliyan 777 da ya tashi daga Abuja ya nufi Kaduna ya wuce Zariya.
Gwamnatin tarayya dai ta hannanta kwangilar rukunin aikin hanyar sashi na biyu ga kamfanin Infiouest a kan kudi naira Biliyan 525, biyo bayan soke kwantiragin farko da aka bai wa kamfanin Julius Berger Plc, sakaman rashin jituwa da aka samu kan karin kudaden kwangilar.
- Bai Wa Shanu Guba: Sojoji Sun Shiga Tsakani Domin Dakile Yunkurin Ramuwar Gayya A Filato
- ‘Yansanda Sun Kama Mutane 157, Sun Ƙwato Bindigu Da Miyagun Ƙwayoyi A Kano
Ministan ayyuka, Injiniya Dabid Umahi, shi ne ya bayar da wa’adin a lokacin kaddamar da zango na biyu na aikin hanyar wanda ya gudana a garin Jere da ke karamar hukumar Kagarko a Jihar Kaduna.
An tsara aikin don kammalawa tare da shingen karfafawa na kankare kuma ana sa ran za a kammala shi cikin lokacin da aka ware.
Umahi ya yaba wa Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, bisa goyon baya da hadin kai da yake bai wa gwamnatin tarayya wajen ganin an kammala aikin a kan lokaci.
Ya yi bayanin cewa aikin hanyar mai nisan kilomita 700 da ya tashi daga Abuja ya wuce Kaduna ya nufi Zariya zuwa Kano zai yi matukar rage yawan aukuwar hatsari da cunkoson ababen hawa da zarar aka kammala shi.
“Muna da sashe na 1, 2, 3. Sashi na 1 yana Abuja da Neja, sashe na 3 kuma yana Kano, kuma sashen Kano da ke tsakanin Zariya zuwa Kano tuni Julius Berger ya kammala shi, don haka gaba daya titin, 350, shi ne kilomita 240 da Julius Berger ya kammala.
“Sauran kilomita 140 da 2, 240 ta 2 shi ne 480. 140 ta 2 shi ne 280. Amma shugaban kasa ba kawai kammala 280 din ne ba, ya ma kara kusan sama da kilomita 11 a rukunin aikin da ke Kano domin jan titin har zuwa filin sauka da tashin jirage na kasa da kasa ta Malam Aminu Kano. Kuma aikin na ci gaba da gudana a halin yanzu, tare da sauran dan kadan da ya rage a Jihar Kano.
“Shugaban kasa ya kuma bayar da umarnin a sanya turakun hasken wuta mai amfani da haske rana gaba daya. Kuma zuwa yau, shugaban kasa ya bayar da kwangilar karasa sashi na 1 da na 3 na aikin mai nisan kilomita 118 a kan kudi naira biliyan 252.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp