Gwamnatin Nijeriya ta ce ta fara biyan naira 35,000 ga ma’aikatan ta wata biyar don rage radadin cire tallafin man fetur tun karshen watan Mayun 2025.
Wannan na zuwa ne a yayin da gwamnatin tarayya ta fayyace zare da abawa kan aiwatar da tsarin mafi karancin albashi na naira 70,000 ga dukkanin ma’aikatanta.
- Gwamnatin Kano Ta Ƙaryata Karɓo Bashin Dala Miliyan 6.6
- Gwamnatin Tarayya Ta Dukufa Wajen Karya Farashin Kayan Abinci – Minista
Daraktan yada labarai a ofishin Akanta Janar na tarayya, Bawa Mokwa, shi ne ya tabbatar da hakan a hirarsa da ‘yan jarida a ranar Litinin bayan dawowar hutun babban Sallah.
Idan za a iya tunawa da a ranar Juma’ar da ta gabata ne mai magana da yawun kungiyar kwadago, Benson Upah, a hirarsa da gidan talabijin na Arise ya soki gwamnatin Shugaban kasa Bola Tinubu kan jinkirin biyan tallafin rage radadin da alawus-alawus.
Upah ya koka kan cewa gwamnatin Tinubu ta yi watsi da kula da walwala da jin dadin ma’aikata duk kuwa da halin matsin tattalin arziki da na rayuwa da ma’aikata ke kara fuskanta.
Da yake maida martani, Mokwa ya ce gwamanti ta fara biyan bashin tallafin rage radadin ga ma’aikata. Ya ce za a ci gaba da biyan kudin ne kashi-kashi har zuwa nan da watanni hudu masu zuwa.
“Mun fara biyan bashin nira 35,000 ga ma’aikata. Illar kawai wasu ma’aikatu da suka kasance masu cin kashin kansu da suke biyan tallafin kai tsaye, misali, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa.
“Amincewa da tallafin naira 35,000 ga ma’aikata shi ne mafita ta wucin gadi da gwamnatin tarayya ta yi kafin amincewa da mafi karancin albashi na naira 70,000.
“Wannan ya faru a cikin watanni biyar, amma kungiyar kwadago ta ce ba a fara biya a kan lokaci ba, yanzu kenan akwai bashin watanni biyar.
“A cikin tallafin na watanni biyar, mun biya na wata guda. Yanzu haka tallafin watanni hudu ne suka rage, kuma za a biya su daki-daki,” ya shaida.
Kazalika, Mokwa ya fayyace zare da abawa da cewar gwamnatin tarayya ta fara biyan albashi mafi karanci ga dukkanin ma’aikatu, rassa da sashi-sashi na gwamnatin tarayya.
“Dangane da biyan albashi mafi karanci kuwa, an aiwatar da shi ga dukkanin ma’aikatu,” ya kara tabbatarwa.
Idan za a tuna dai a watan Yuli ne Shugaban kasa Tinubu ya sanya hannu kan dokar mafi karancin albashi.
Sai dai, duk da amincewa da mafi karancin albashi, har yanzu akwai korafe-korafe kan cikakken aiwatar da shi daga jihohi da kuma tarayya baki daya kusan shekara guda kenan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp