Ministan kudi kuma mai kula da tattalin arzikin Nijeriya Wale Edun, ya ce gwamnatin tarayya za ta fara sayar da danyen mai ga Dangote da sauran matatun man kasar nan a farashin Naira daga ranar 1 ga Oktoba, 2024.
Ministan ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a taro na biyu na taron kwamitin aiwatarwa kan batun sauya farashin sayar da danyen mai zuwa Naira da shugaba Bola Tinubu ya kafa.
- Peng Liyuan Ta Gana Da Uwar Gidan Shugaban Vietnam
- NYSC Ta Kori Ƴan Bautar Ƙasa 54 Masu Takardun Bogi
Sanarwar ta ce, an kuma samar da sabbin bayanai kan matatun mai na Fatakwal da Dangote, inda ake sa ran za a samu karin yawan man da ake samarwa daga watan Nuwamba na shekarar 2024. Sai dai, sanarwar ba ta bayyana lokacin da matatar man Fatakwal za ta fara aiki ba.
Kamfanin man fetur na Nijeriya (NNPCL) ya dage ranar fara aikin matatar mai ta Fatakwal a karo na shida tun bayan da Mele Kyari ya zama shugaban kamfanin.