Gwamnatin Kano, ta kudiri aniyar gina gidaje ga mutanen da ambaliyar ruwa ta rushe wa muhalli a jihar.
Wannan na cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Alhamis.
- Tallafin Daular Larabawa Ya Iso Nijeriya Ga Masu Ambaliya
- Ambaliyar Ruwa Ta Katse Hanyar Maiduguri Zuwa Damboa
Ya ce gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf, ya ce wannan tallafin gidajen zai taimaka wajen rage raɗaɗin da ambaliyar ruwan ta haddasa ga magidanta a jihar.
Gwamnan, ya ce gwamnatinsa na aikin hadin gwuiwa da ma’aikatar jin-ƙai domin samar da abinci da wasu kayayyaki ga mutanen da lamarin ya shafa.
Ambaliyar ruwa a daminar bana dai ta ɗaiɗaita miliyoyin mutane a Nijeriya, lamarin da ya sanya mutane da dama komawa zama a sansanin ‘yan gudun hijira.
A baya-bayan nan, ambaliyar ruwa ta shafe wasu sassa na birnin Maiduguri da ke Jihar Borno, sakamakon ɓallewar madatsar ruwa ta Alom da ke jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp