Gwamnatin tarayya a ranar Alhamis ta shaida cewar za ta kashe naira biliyan ashirin da biyu da digo hudu (N22.4billion) wajen ciyar da Fursunoni da suke gidajen gyaran hali a fadin kasar nan a cikin shekarar 2023.Â
Kan hakan, Fursunonin kasar nan za su ci abincin biliyan sama da 22 a cikin shekara guda.
Babban Sakataren ma’aikatar kula da harkokin cikin gida, Dakta Shuaib Belgore, shi ne ya shaida hakan a wajen taron kwana biyu kan hanyoyin da za a bi wajen rage cinkoson Fursunoni da garambawul ga hanyoyin gudanarwa da ke gudana a Abuja.
Belgore ya ce, kudin an shigar da shi cikin kasafin kudin 2023.
Ya ce, akwai dumbin yawan karuwan Fursunoni da ake fama da su a gidajen yarin kasar nan ta yadda kashi 80 cikin 100 na Fursunonin su na zama jiran shari’a ne.
A cewarsa akwai gidajen yari guda 244 a fadin kasar nan, da ke dauke da Fursunoni guda 75,507 wanda a bisa hakan ya janyo wasu da dama daga cikinsu suke fama da cunkoso.
A cewarsa, adadin Fursunonin ya kai ga Maza 73,821 yayin da ake da mata 1,686 da suke matsayin Fursunoni a gidajen yari daban-daban a fadin kasar nan.
A fadinsa, daga cikin adadin Fursunonin 75,507, 52,436 su na zaman jiran shari’a ne kawai, yayin da 23,071 aka zartar musu da hukunci kan laifukan da kotuna suka kamasu da aikatawa, sannan akwai wadanda aka yanke musu hukuncin kisa su 3,322.